in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tuntubar al'adun kabilu daban daban na kasar Sin a ranar yara ta duniya
2010-06-07 15:57:45 cri

Ran 1 ga wannan wata ta kasance ranar yara ta duniya, wadda kuma rana ce da yara ke sa ran samun alheri sosai a kai a cikin shekara guda. Yanzu sakamakon kyautatuwar zaman rayuwar jama'a, sanya sabbin tufafi da cin abinci mai dandano kadai ba su iya ba da sha'awa sosai ga yaran kasar Sin. Sabo da haka, dimbin makarantun firamare da na sakandare na kasar Sin su kan shirya bukukuwan tunawa da ranar yara bisa ra'ayin jin dadin zaman rayuwar da ya shafi al'adu. To a cikin shirinmu na yau, bari mu leka makarantar firamare ta 'yan kabilar Hui ta unguwar Dongcheng ta birnin Beijing domin yin shagalin ranar yara tare da 'yan makaranta na kabilu daban daban.

An kafa makarantar firamare ta 'yan kabilar Hui ta unguwar Dongcheng ta birnin Beijing ne a shekaru 80 na karnin da ya gabata, tare da nufin samar da damar karatu ga yara musulmai da ke zaune a kusa. Bayan samun bunkasuwa a cikin shekaru da dama da suka gabata, yanzu makarantar ta riga ta zama wata makarantar zamani da ke da malamai da 'yan makaranta fiye da 500 daga kabilu 9 na kasar Sin. Bao Yuhong, shugabar makarantar wata musulma ce, kuma ta gaya wa wakiliyarmu cewa, ita wata 'yar karamar kabila ce, hadin gwiwa da kuma samun jituwa a tsakanin kabilu daban daban sun burge ta sosai. Don haka a matsayinta ta wata makarantar kananan kabilu, makarantar firamare ta 'yan kabilar Hui ta unguwar Dongcheng ta kan dora muhimmanci sosai kan koyar da ilmin da ya shafi kananan kabilu da al'adunsu domin yara 'yan kabilu daban daban su girma a cikin yanayin hadin gwiwa da samun jituwa. Madam Bao Yuhong ta bayyana cewa,

"Muna gudanar da harkokin makarantarmu ne bisa ra'ayin nuna girmamawa da yin hakuri da juna a cikin yanayin kasancewar al'adu iri daban daban, wanda kuma sakamako ne da malamanmu muka samu tare. Ana iya samun al'adu iri daban daban ko a kasar Sin ko a sassan duniya, muna fatan ta hanyar samun ilmi a makarantar 'yan kabilar Hui ta Dongcheng, 'yan makarantarmu za su iya hadin kai da nuna girmamawa kana da yin hakuri da sauran mutane."

Sakamakon kasancewar irin wannan ra'ayi ta fuskar gudanar da harkokin makaranta, kafin zuwan ranar yara wato ran 1 ga watan Yuni, makarantar 'yan kabilar Hui ta unguwar Dongcheng ta shirya wani biki da aka yi wa lakabin "gaji al'adun gargajiya na kabilun kasar Sin domin jin dadin ranar yara". Ana fatan 'yan makarantar za su iya jin dadin al'adun gargajiya na kabilun kasar Sin a cikin halin annashuwa.

Da shigar wakiliyarmu kofar makarantar 'yan kabilar Hui ta unguwar Dongcheng da ke da halin musamman na ginin Islama, kide-kide masu dadin ji sun jawo hankalinta sosai. Bayan da ta isa filin wasa, abin da ya bayyana a gabanta ya shiga cikin zuciyarta, 'yan makarantar da ke sanye da kyawawan tufafin kananan kabilun kasar Sin suna yin rawar gora, wato wasu 'yan makaranta suna kasa suna motsa gorori, yayin da wasu daban suna ketara gororin suna rawa. Sauran malamai da 'yan makarantar da ke filin wasa kuwa suna yin tafi, lallai sun ji dadi kwarai da gaske.

Ban da rawar kananan kabilun kasar Sin, 'yan makarantar sun nuna tufafin kananan kabilu, da yin kide-kide da kayayyakin kida na gargajiya, da yin abubuwan fasaha da hannu, kana da nuna al'adun gargajiya na kananan kabilu a kan allo. Ma Tianyu, musulmi dan kabilar Hui kuma wani dan makarantar ya gaya wa wakiliyarmu cikin farin ciki, cewar bikin tunawa da ranar yara ta bana na da ban sha'awa, ya karu sosai. Yanzu ban da kabilar Hui, ya kara fahimtar sauran kabilu na kasar Sin. Ya ce,

"A ganina, bikin na da matukar kayatarwa, abokan karatuna sun sanya tufafin kabilu masu dimbin yawa, lallai suna da kyan gani sosai. Ban da wannan kuma ta hanyar shiga bikin, na karu kwarai, na san cewa, 'yan kabilar Zhuang ba su cin kwayayen kaji, salla mafi muhimmanci ga 'yan kabilar Dai kuma ita ce sallar zubar da ruwa."

Nuna al'adun kabilu a kan allo abu ne da ya jawo hankalin mutane sosai a gun wannan bikin nune-nune da makarantar firamare ta 'yan kabilar Hui ta Dongcheng ta shirya. Wasu 'yan makarantar da ke sanye da tufafin gargajiya na kabilu daban daban sun tsaya a gaban allon nune-nune da suka yi da kansu, da kuma gabatar wa abokan karatunsu da al'adu da ilmi na kabilu 56 na kasar Sin. A wasu lokuta ma, sun yi tambayoyi kan wadannan kabilu domin 'yan makaranta su amsa. Ba kawai abubuwa masu ban sha'awa sun jawo hankalin 'yan makaranta ba, har ma sun sa bakin da suka halarci bikin bisa gayyatar da aka yi musu sun bayyana da takensu a gaban allon. Yayin da yake tabo magana kan wannan bikin nuna al'adun kabilu na kasar Sin, Arken Hadir, mataimakin babban edita na kamfanin buga littattafai kan kabilu na birnin Beijing ya nuna babban dan yatsansa. Ya ce,

"Ya kamata a fahimci kyan surar kasar Sin da al'adun kabilu 56 na kasar tun lokacin kuruciya. Kabilu 56 su ne suka kago al'adar kasar Sin tare. Ya kamata a koyar wa yara wannan ra'ayi ta hanyar shirya bukukuwan al'adu. Dazun nan wasu yara sun gabatar da tufafin kananan kabilu kana da halin musamman na yankunan da 'yan kananan kabilu ke kasancewa a ciki. Irin wannan mu'amalar da ke tsakanin yara tana da kyau sosai, yara za su fahimci ilmin cikin sauki."

Ba kawai fahimtar al'adu kan kananan kabilu za ta kara ilmin da yara ke da shi, da kuma sa kaimi ga yara 'yan kabilu daban daban wajen kara fahimtar juna da nuna girmama juna kana da samun jituwa a tsakaninsu ba, hatta ma za ta taka muhimmiyar rawa ga gadar wadannan al'adun gargajiya. Bao Yuhong, shugabar makarantar firamare ta 'yan kabilar Hui ta Dongcheng ta bayyana cewa, yanzu sakamakon canzawar zamani, wasu al'adun gargajiya na kasar Sin musamman ma wasu fasahohin gargajiya suna dab da bata Don haka, yayin da suke shirya bikin murnar ranar yara ta bana, sun gayyaci magajin Rongbutang, wani kamfanin kera kayayyakin wasa na yara da ke da tarihin fiye da shekaru 100, kana da mai rike da fasahar yanka takardu da almakashi domin koyar wa yara yadda za a kera kayan wasa na yara da kuma yanka takardu, da nufin kara sha'awar da za su nuna wa fasahohin gargajiya na kasar Sin, ta haka za a samu masu gadon al'adun gargajiya na Sin a nan gaba.

A filin wasa, wakiliyarmu ta gano cewa, Li Lan, wata tsohuwa mai shekaru 71 a duniya da ke rike da fasahar yanka takardu da almakashi tana koyar wa 'yan makaranta yadda za a yanka taurari masu kusurwoyi 5 da takardu da almakashi. Bayan da ta ga 'yan makarantar sun samu nasarar yanka takardun, ta yi murmushi. Kuma ta gaya mana cewa,

"Wasu fasahohin gargajiya na kasar Sin sun riga sun kare, wannan abin bakin ciki ne. Ya kamata yara su gaje su da kuma yada su. Ko da yake na tsufa, amma zan yi iyakacin kokarina domin koyar musu fasahar yanka takardu da almakashi."

A kan fuskokin yara masu murmushi, wakiliyarmu ta gano cewa, lallai sun ji dadi sosai a ranar yara ta bana. Ana fatan za yi ta tunawa da wannan rana har abada sakamakon shiga wannan bikin nuna al'adu na kananan kabilu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China