in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani dangane da taron koli kan tsaron nukiliya
2010-04-13 09:34:22 cri
Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Yau sauran kwanaki 14 ne a kaddamar da bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai. Ko kuna sha'awar sheda wannan gagarumin biki? Ko kuna so ku kawo ziyara a nan kasar Sin? Muna fatan za ku ci gaba da aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayoyinku game da bikin baje koli na birnin Shanghai. To, yanzu bari mu fara karanta wasu wasikun da muka samu daga wajenku. Da farko ga wannan sako daga malam Joda Musa a tarayyar Nijeriya, inda ya rubuto mana ta yanar gizo cewa, "Bayan gaisuwa mai tarin yawa, da fatan dukkan ma'aikatan wannan gidan radio mai farin jini da gamsarwa suna cikin koshin lafiya. Bayan haka na rubuto muku wannan wasika ce domin sada zumunci, kuma in nuna muku sha'awata a gare ku da shirye-shiryenku. Allah ya bar zumunci, amin."

To, mun gode, malam Joda. Muna farin ciki sosai da ka ci gaba da rubuto mana domin bayyana sha'awarka. Abubuwan da ka bayyana mana suna kara mana kwarin gwiwa. Ba shakka, a nan gaba za mu kara kokarin domin samar da shirye-shirye masu kyau. Da fatan za ka ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu. Mun gode.

Bayan haka, malam Zouladeyni Abdou a birnin Agadas, Jamhuriyar Nijar ya rubuto mana cewa, "Bayan gaisuwa mai tarin yawa da fatan alheri zuwa ga sashen hausa na radiyon CRI cewa, a gaskiya muna jin dadin shirye-shiryenku, kuma ni ba bako ba ne wajen sauraronku, amma bako ne wajen aiko muku da wasika. Ina son kulla zumunta da ku, kuma ku sanya ni a cikin masu sauraronku a yau da kullun in Allah ya so!"

To, mun gode, malam Abdou. Muna farin ciki da samun sako daga wajenka, tare da yin alfahari da samun amincewarka. Lalle muna bukatar goyon baya daga dukkan ku masu sauraronmu. Da fatan za ku kara rubuto mana ta wasiku ko ta yanar gizo domin ba da shawarwari masu kyau. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin!

To, sakon malam Abdou ke nan. Sai wani sako daga malam Muhmmed Awaisu dake jihar Bauchi ta Nijeriya, inda ya bayyana cewa, "Assalamu alaikum gidan radyion kasar Sin! Bayan gaisuwa mai yawa, da fatan za ku ci gaba da shirye-shiryenku masu kayatarwa, kamarsu kananan kabilun kasar Sin, da zabi sonka, da labarai dangane da nahiyar Afirka da dai sauransu."

To, mun gode, malam Awaisu. Ko shakka babu kana sauraronmu a yau da kullum, har ma ka zabi shirye-shiryenmu a matsayin wadanda suka fi burge ka. Lallai dukkan ma'aikatanmu na sashen Hausa na CRI muna iyakacin kokari, da fatan masu sauraronmu za ku samu ilmi da kayatarwa da nishadantarwa da dai sauransu. Yanzu ka bayyana mana amincewarka ga shirye-shiryenmu. Muna fatan za ka ci gaba da mai da hankali da kuma ci gaba da shiga a ciki. Sai mun ji daga gare ka da ma sauran masu sauraronmu, amin.

To, bayan wannan sakon da muka samu daga malam Muhmmed Awaisu a Nijeriya, sai malam Usman Rabilu a Gombe, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Na ji an ce yanzu batun Nukiliya ya fi jawo hankalin jama'ar kasa da kasa, ko ba haka ba?"

E, haka ne, malam Usman. A ran 12 da ran 13 ga wata, an yi taron koli kan tsaron nukiliya a birnin Washington na kasar Amurka bisa kiran da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi. Kuma wannan ne muhimmin taro a tsakanin bangarori da dama, wadanda suka dora muhimmanci a kansa sosai da sosai. Shugabanni da wakilai na kasashen duniya sama da 40 da masu ruwa da tsaki daga MDD da hukumar IAEA da kungiyar tarayyar Turai da dai sauransu duka sun halarci wannan taro. Alexandra Toma, masani a fannin batun nukiliya dake aiki a asusun mu'amala na kasar Amurka ya bayyana cewa, dalilin da ya sa kasar Amurka ta jagoranci wannan taro shi ne, a ganinta yanzu ta'addanci ya riga ya zama wata babbar barazana ga kasar Amurka, har ma duk duniya baki daya. Ga abin da ya ce,

"Mutane sun sanya ra'ayinsu a kan makaman nukiliya a sakamakon harin da aka kai a ran 11 ga watan Satumba na shekarar 2001 a kasar Amurka. Masana a harkokin tsaro sun gano cewa, idan 'yan ta'adda suka sayi ko saci ko kuma samar da makaman nukiliya, wannan zai kawo babbar barazana ga Amurka da 'yan kawancenta. Kuma yanayin tsaro na duniya yana fuskantar manyan kalubaloli guda biyu, wato ta'addancin nukiliya da bazuwar makaman nukiliya. Duk da haka kuwa, ana iya daukar matakai domin yin rigakafi da kuma yaki da su."

A gun taron koli kan tsaron nukiliya, an yi shawarwari a kan yadda za a tabbatar da tsaro kan sinadaren nukiliya da dai sauransu. Bisa farfado da harkar samar da wutar lantarki ta amfani da karfin nukiliya da bunkasa shi, da kara yin amfani da sinadaren nukiliya da fasahohin nukiliya, yiwuwar baza sinadaren nukiliya ta karu. A sa'i daya, ana cikin mawuyacin halin ta fuskar tsaro a duniya. Da kyar za a iya kyale danyun ayyukan da 'yan ta'adda suke yi na neman samu da yin jigilar sinadaren nukiliya ba bisa doka ba, har ma na kai hare-hare a kasashen duniya. Game da wannan lamari, Matthew Bunn, masani a fannin manufofin zaman al'umma na jami'ar Harvard ta Amurka ya bayyana cewa,

"Kamata ya yi a dauki matakai a matsayin kasa da kasa nan take. Makasudin gudanar da taron kolin nan shi ne fara kokari a matakin kasa da kasa, da kuma kara saurin hakan. Shugabanni na kasa da kasa sun yi shawarwari a gun taron kolin a kokarin kiyaye tsaron nukiliya cikin sauri. Kuma abin dake gaba da komai shi ne fahimtar da wadannan shugabanni da su gano cewa, lallai ta'addancin nukiliya yana kawo barazana, kuma dole ne shugabannin su dauki matakai nan da nan a kokarin tabbatar da tsaron nukiliya."

To, jama'a masu karanta, yanzu bayani ke nan kan tambayar malam Usman Rabilu, da fatan ka ga ka gamsu da shi.

Bayan haka, a kwanan baya, masu sauraronmu da yawa sun aiko mana da wasiku, kamar malam Abdullahi Garba a tarayyar Nijeriya, da malam Dan'juma Yahaya a Kaduna, tarayyar Nijeriya, da malam Nassirou Souleye, dan Nijer dake kasar Italiya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki da sakwannin naku. Da fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu na Amsoshin Wasikunku. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China