in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar harsunan mahaifa ta kasashen duniya
2010-02-20 17:13:39 cri
Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. To, kamar yadda muka saba, da farko za mu karanta wasu wasiku daga wajen masauraronmu. Ga wannan daga malam Maikudi Abdul daga jihar Nijer, tarayyar Nijeriya, ya ce, "CRI ita ce gidan radiyo da ta fi muhimmanci a gare ni. Ina jin dadin shirye-shiryenku kwarai da gaskiye. shirye-shiryenku sun kasance masu ilmartarwa da fadarkarwa da kuma shakatarwa."

To, mun gode, malam Maikudi Abdul. Kamar yadda ka bayyana a sakonka, kai da duk sauran masu sauraronmu kuna da muhimmanci a gare mu, muna ta kokarin samar da shirye-shirye masu kyau sabo da ku. Kuma mun samu zumunta da kwarin gwiwa da gaskatawa da sauran abubuwa masu dajara da yawa daga wajenku. Mun gode muku kwarai da gaske. Da fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

To, sakon malam Maikudi Abdul ke nan. Bayan haka, malam Ibrahim Gyaranya a Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Na tambayi adreshinku na yanar gizogizo ta internet, amma har yanzun ba ku turo mini ba."

To, malam Ibrahim, kada ka damu. Yanzu za mu ba da amsa. Adreshinmu na yanar gizo ta internet shi ne www.hausa.cri.cn, kuma mun yiwa shafinmu na internet kwaskwarima a kwanan baya bisa shawarwarin da masauraronmu suka bayar masu kyau. Muna fatan za ka huce, da kuma dinka duba shafinmu na internet. Allah ya bar mu tare, amin.

Bayan haka, a kwanan baya, malam Muhammed Bako daga Katsina, tarayyar Nijeriya ya aiko da wani sako cewa, "Don Allah ko za ku ba ni wani bayani a kan ranar harsunan mahaifa ta kasashen duniya?" To, ba shakka, malam Muhammed, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya, da fatan kana sauraronmu.

A shekarar 1952, jama'ar dake yankin gabashin kasar Pakistan sun yi zanga-zanga a kokarin samar da harshen Bangladesh a matsayin daya daga cikin harsunan gwamnatin kasa. A ran 21 ga watan Febureru na wannan shekara, an harbe masu zanga-zanga 5. A sabili da haka, a shekarar 1999, kungiyar UNESCO ta MDD ta samar da ranar 21 ga watan Febureru na kowace shekara a matsayin ranar harsunan mahaifa ta kasashen duniya, a yunkurin tunawa da wadannan jama'ar yankin gabashin Pakistan da suka sadaukar da ransu domin neman yin amfani da harshen mahaifa. Makasudin kafa wannan rana shi ne taimakawa jama'ar kasa da kasa da su fahimci halin al'adun harsunan mahaifa na kabilu daban daban na kasashen duniya suke ciki a yanzu, a kokarin sa kaimi ga bunkasa harsuna da al'adu a fannoni iri-iri.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, kawo yanzu dai akwai harsuna sama da dubu 7 a duniya. Amma mutane kashi 97 cikin kashi dari na duk dan adam suna amfani da harsuna kashi 4 cikin kashi dari na dukkansu. Kuma ana yin amfani da harsuna kasa da kashi daya bisa kashi hudu a makarantu da yanar gizo ta internet. Wato harsuna sama da dubu daya sun rasa damar taka muhimmiyar rawa a fannin tarbiyya da kafofin yada labaru da littattafai da zamantakewar al'umma. Yawan harsunan kasashen duniya sama da kashi 50 cikin kashi dari zai bace, sai aka dauki kwararan matakai nan take.

Harshe wani irin kayan aiki ne mai daraja kwarai, shi ya sa kiyaye harsunan mahaifan kasashen duniya yana da ma'ana sosai. Wasu kasashe sun riga sun yi nasara wajen kiyaye harsunan kananan kabilu, kamar harshen Kymric da na Catalan da na Indiya a Canada da dai sauransu. Masanan kungiyar UNESCO ta MDD suna zaton cewa, kamata ya yi 'yan adam su kara karfin kiyaye harsunan mahaifansu, kamar kafa harsunan gwamnatin kasa, da tsara littattafan karatu da harsuna da dama, da kyautata tsarin ajiye bayanan harsuna da yin amfani da su yadda ya kamata. A halin yanzu, kara yin amfani da harsuna daban daban a yanar gizo ta internet shi ma wata muhimmiyar hanya ce wajen kiyaye harsunan mahaifa.

A shekarar 2006, kungiyar UNESCO ta gudanar da aikin tunawa da ranar harsunan mahaifa ta kasashen duniya a birnin Beijing na Sin a karo na farko. Daga bisani, a kowace shekara ana gudanar da bikin tunawa da wannan rana a kasar Sin. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, Sin ta yi ayyuka da yawa wajen kiyaye harsuna da kalmomin kananan kabilun kasar, kamar koyar da dalibai da harsunan kananan kabilu, da kafa dandalin ba da hidimomi wajen kiyaye ikon mallakar ilmi na harsunan kananan kabilu da dai sauransu, ta yadda za a girmama da yada al'adu ta hanyar kiyaye wadannan harsuna.

To, jama'a masu karanta, bayani ke nan kan tambayar malam Muhammed Bako. Da fatan ka ji ka gamsu da shi.

Bayan haka, a kwanan baya, masu sauraronmu da yawa sun aiko mana da wasiku, kamar malam Muhammed Musa daga Nijeriya ta yanar gizo, da malam Yusuf Ali daga Bauchi, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki. Da fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu na Amsoshin Wasikunku. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu. To, jama'a masu sauraro, muna nan muna tare da ku a ko da yaushe, da fatan za mu samu karin sakwanni a mako mai zuwa. Yanzu iyakacin shirinmu ke nan, ni Fatima ke cewa da alheri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China