in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kiyaye ire-iren halittu masu rai a kasa da kasa a bana
2010-02-01 15:19:48 cri
Jama'a masu karanta, yaya kuke? Yaya aiki? Muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. A makon jiya, masu sauraronmu da dama sun rubuto mana wasiku domin nuna gaishe-gaishe da ba da shawarwari masu kyau, ciki har da malam Salisu Dawanau daga tarayyar Nijeriya, a cikin sakonsa ya bayyana cewa,

"Masu iya magana kan ce, 'yawan gaisuwa tafi yawan fada'. Wannan magana haka take, babu tantama. Saboda haka, wannan wasika tawa ta gaisuwa ce zuwa gare ku baki daya."

To, mun gode, malam Salisu. Muna maka gaisuwa tare da fatan alheri, da fatan Allah ya saka maka da alherinsa. A nan gaba, muna fatan za ka ci gaba da sauraronmu, da ba da shawarwari masu kyau. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Sakon malam Salisu ke nan. Bayan haka, malam Sanusi Isah Dankaba daga Nasarawa, tarayyar Nijeriya, ya bayyana mana cewa,

"Shin da gaske ne sashen hausa za ku shirya wata gasar kacici kacici dangane da lardin Sichuan? Idan haka ne, yaushe za ku fara wannan gasa kuma ina tambayoyin wannan gasar suke?"

To, malam Sanusi, a hakika dai, mun riga mun fara wannan gasar kacici-kacici mai suna "Ina son in je lardin Sichuan ta Sin". Kuma ana iya samun tambayoyin gasar a shafinmu na internet. Masu sauraronmu da dama sun riga sun shiga ciki, har ma wasu sun riga sun aiko mana da amsoshinsu, kamar malam Salisu Dawanau da muka ambace shi a dazun nan da dai sauransu. A sabili da haka, muna fatan, malam Sanusi, za ka shiga gasarmu cikin hanzari, a kokarin samun kyautar da tashar CRI za ta bayar. Allah ya kara taimakawa, amin.

To, jama'a masu karanta, a cikin shirinmu na baya, mun taba gaya muku cewa, ranar 14 ga wata ranan nan ce ta farko ta sabuwar shekarar 2010 bisa kalandar noma ta kasar Sin. Sinawa su kan yi gagarumin biki domin murnar zuwan sabuwar shekara a wannan rana. Kowa kan sa sabbin tufaffi tare da gaida juna. Ko kuna sha'awar wannan biki? Ko za ku mika gaisuwa da fatan alheri ga abokanku Sinawa? Muna fatan za ku kara aiko mana da sakwanni domin yin murna tare da mu, mun gode.

Bayan haka, kwanan baya, malam Ibrahim Gyaranya daga Bauchi, tarayyar Nijeriya, ya aiko da wani sakon cewa, "Na ji an ce, bana shekara ce ta kula da ire-iren halittu masu rai ta duniya, ko ba haka ba?"

E, haka ne, malam Ibrahim. A shekarar 2006, babban taron MDD ya zartas da wani kuduri cewa, za a mayar da shekarar 2010 a matsayin shekara ta kula da ire-iren halittu masu rai ta duniya, a kokarin fadakar da muhimmanci na kiyaye ire-irensu ga jama'ar kasa da kasa, da sa kaimi ga bangarori daban daban da su dauki matakai cikin sauri. Takenta shi ne "Ire-iren halittu rayuwa ne, har ma rayuwarmu".

A sakamakon haka, za a kaddamar da tarurruka da dandalin tattaunawa da dai sauransu a duk fadin duniya. Kuma za a kai matakin koli a watan Satumba na bana. A daidai wannan lokaci, babban taron MDD zai gudanar da wani taro bisa matsayin koli, inda shugabannin kasa da kasa za su yi shawarwari a kan kiyaye ire-iren halittu masu rai da tabbatar da amfaninsu na yaki da sauyawar yanayi. Kuma za a bayar da rahoton da za a samu a wannan taro ga taron kasashe don rattaba hannu kan yarjejeniyar kula da ire-iren halittu a karo na 10 da za a gudanar a birnin Nagoya na kasar Japan. Bugu da kari, wadannan kasashe za su tsara wani sabon shiri domin tabbatar da wannan yarjejeniya.

Yarjejeniyar kula da ire-iren halittu masu rai, wata yarjejeniyar duniya ce ta kiyaye albarkatun halittu. Bisa jagorancin hukumar kula da harkokin muhalli ta MDD, an samar da kuma zartas da ita a shekaru 90 na karnin da ya gabata. Makasudinta shi ne kula da duk dabbobi da tsire-tsire da suke shude, a kokarin kiyaye ire-irensu a duniya. Bisa wannan yarjejeniya, shugabannin kasa da kasa sun alkawarta cewa, kafin shekarar 2010, za su kyautata halin da ake ciki na rasa ire-iren halittu masu rai cikin sauri. Kawo yanzu dai, kasashe 193 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Ire-iren halittu masu rai na nufin duk halittu dake rayuwa a duniya, wadanda suke hada da dabbobi da tsirrai da kwayoyin halittu, wato microbe da muhalli da dai sauransu. Masana sun kiyasta cewa, a sakamakon ayyukan dan Adam da sauyawar yanayi dake kara tsananta a yau da kullum, yanzu ire-iren halittu masu rai suna shudewa cikin sauri da ya ninka sau 1000 bisa na kullum. Watakila hakan zai haddasa babbar illa ga lafiyar dan Adam da aikin gona da sha'anin kiwon dabbobi, har ma yana iya yin barazana ga rayuwar dan Adam. Ya zuwa yanzu, gaba daya tsirrai dubu 34 da dabbobi dubu 5.2 suna bakin shudewa a duniya.

To, jama'a masu karanta, yanzu bayani kan nan kan tambayar malam Ibrahim, da fatan ka ji ka gamsu da shi.

Bayan haka, a kwanan baya, masu sauraronmu da yawa sun aiko mana da wasiku, kamar malam Abdullahi Garba daga Nijeriya, da malam Aliyu Baka tsoron Moba daga karamar hukumar Kamba ta jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki. Da fatan za ku ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu na Amsoshin Wasikunku. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu. To, jama'a masu sauraro, muna nan muna tare da ku a ko da yaushe, da fatan za mu samu sakonka a mako mai zuwa. Yanzu iyakacin shirinmu ke nan, ni Fatima ke cewa da alheri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China