in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan shahararren dan jarida Israel Epstein
2009-12-28 15:32:24 cri
Marigayi Israel Epstein, wani shahararren dan jarida dake samun karbuwar jama'ar Sin kwarai, kuma yana daya daga cikin aminan Sin 10 daga ketare, wadanda suka fi taimakawa kasar Sin a cikin 'yan shekaru 100 da suka wuce. Kwanan baya, matarsa Huang Huanbi ta yi bakunci a gidan rediyon kasar Sin, inda ta bayyana wa wakilinmu da abubuwan da suka abku a cikin zaman rayuwar mijinta na ganin samun bunkasuwar kasar Sin.

An haifi Israel Epstein a shekarar 1915 a wani iyalin Yahudawa dake birnin Warsaw na kasar Poland. An taba cafke mahaifansa da kuma kore su sabo da shiga jiki a yake-yaken juyin juya hali. Yayin da shekarunsa suka kai 2 da haihuwa, mahaifansa sun zo kasar Sin tare da shi. Mista Epstein ya taba bayyana cewa, mafi yawan mutane sun fara son duniya sabo da son kasarsu, amma a matsayinsa, ya fara son kasa sabo da son duniya baki daya. Matarsa Huang Huanbi ta bayyana cewa,

"Ya girma a kasar Sin. Kuma a lokacin, ba shi da shedan zama dan kasa. A sabili da haka, Epstein ya bayyana cewa, ya fara son kasa sabo da son duniya baki daya. Da karshe kuma, ya zama dan kasar Sin, har ma ya shiga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ya sadaukar da kansa ga kasar ba tare da yin da-na-sani ko kadan ba."

Israel Epstein ya taba karatu a birnin Harbin da Tianjin da sauransu, inda ya ga danyun ayyuka da sojoji masu kawowa kasar Sin hare-hare suka yi. A kai a kai, ya fara jin tausayi ga kasar Sin. A matsayin wani dan jarida mai ba da labaran yake-yake, ya je fagen yake-yake da kansa, a yunkurin ba da labarai dangane da jaruntakar sojojin kasar Sin.

Domin gabatar da hakikanin halin da ake ciki a yankunan samun 'yancin kai ga duniya tun da wuri, ya rubuta labarai a kasar Amurka domin kaucewa danyun ayyukan da jam'iyyar Kuomintang ta yi. A daidai wannan lokaci, shi da matarsa sun jagoranci mutane da yawa daga sassan daban daban da su yi zanga-zanga, domin nuna rashin amincewa ga Amurka da ta sa hannu a harkokin gida na kasar Sin. Kuma ya fassara wata waka mai suna "Wakar rawayen kogi" daga Sinanci zuwa Turanci domin rera ba tare da fasawa ba.

A shekarar 1951, Israel Epstein ya dawo birnin Beijing na Sin bisa gayyatar tsohon firaministan kasar Zhou Enlai da Song Qingling, domin daukar nauyi na tsara jaridar "Bunkasa kasar Sin", wadda aka fassara da harsuna da dama zuwa kasashe da yankuna sama da dari, a yunkurin bayyanawa duniya sabon halin da ake ciki a kasar Sin cikin lokaci. A daidai wannan lokaci, mista Epstein ya gamu da madam Huang Huanbi. Ga abin da madam Huang ta bayyana,

"Tun daga shekarar 1960, na fara aiki a kamfanin tsara jaridar "Bunkasa kasar Sin" da madam Song Qingling ta kafa. A hakika dai, sunan jaridar shi ne "Farfadowar kasar Sin". Madam Song ta ce, bai kamata a farfado da kasar Sin cikin dogon lokaci ba, dole ne a canza sunanta. Bayan rasuwar madam Song, an canza sunan jaridar zuwa "Kasar Sin a yau". Kuma na fara aiki a nan daga shekarar 1960, yayin da Epstein ya fara daga shekarar 1951. Muna ta yin aiki a kamfani daya."

Nan ba da dadewa ba, Epstein da Huang Huanbi sun yi aure. Madam Huang ta furta cewa, Epstein ya sadaukar da duk rayuwarsa a kasar Sin. ta ce,

"A ganina, abin da ya fi burge shi a zaman rayuwarsa shi ne ya yi intabiyu a Yan'an a shekarar 1944, kamar yadda ya rubuta a cikin littafinsa mai suna "Ganin kasar Sin". A lokacin, jam'iyyar Kuomintang ta sa kangiya a kewayen Yan'an, domin hana buzuwar labarai. Duk da haka kuwa, Epstein ya keta kangiya, ya je Yan'an tare da wasu 'yan jaridar ketare. Ba shakka, jam'iyyar Kuomintang ta damu sosai, ta tura mutane da dama domin kafa kungiyar 'yan jarida daga Sin da ketare. Bayan da ya yi intabiyu a can, Epstein ya ganin sabuwar kasar Sin, mutane suna zuba jini suna yin yaki da sojojin kasar Japan. A sakamakon haka, a cikin littafin, ya rubuto cewa, ya yi imani cewa, jama'ar Sin suna aza tubali ga aikin kafa wata sabuwar kasar Sin a cikin sabuwar duniya a nan gaba."

A lokacin, a matsayinsa na dan jaridar "New York Times" da ta "Times", Epstein ya shiga kungiyar 'yan jaridar Sin da ketare mai kawo ziyara a yankin arewa maso yammacin kasar Sin, wadda ta kai ziyara a Yan'an. A wani bayani, Epstein ya rubuta cewa, manoma za su sami yalwar amfanin gona, yayin da tsofafi da yara suke lami lafiya.

A cikin wata wasikar da ya rubuta wa iyalansa, Epstein ya ce, Na ga wata kasar Sin irin daban. Akwai bambanci tsakaninta da ta jam'iyyar Kuomintang. A wannan kasar Sin, babu yunwa kuma babu kasawa.

Bayan yake-yake, Epstein ya yi marabtar zuwan zaman lafiya tare da jama'ar Sin. A cikin 'yan shekaru 90 na zaman rayuwarsa, Epstein ya shafe shekaru 82 yana nan kasar Sin. Kuma ya ga babbar sauyawar kasar Sin a sabon karnin da ake ciki. Yana jin alfahari sosai, ya ce, a cikin lokacin da tarihi ya tsara, abubuwan da na gamu da su da kuma shiga jiki a jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna da ma'ana sosai.

Matarsa Huang Huanbi ta furta cewa, Epstein ya mai da hankali sosai kan aikin zamanintar da kasar Sin, ga abin da ta ce,

"Da farko, bai fahimta ba. Amma daga bisani, ya gano cewa, ana samun bunkasuwa yadda ya kamata. Ya gaya mini cewa, yanzu kasar Sin ta yi kama da kasashen ketare. Dadin dadawa, ya mai da hankali sosai kan komawar yankin Hongkong. Kuma yana fatan za a samu dinkuwar kasar Sin tsakanin babban yanki da yankin Taiwan tun da wuri. Bayan haka, ya tallafa wani littafi mai suna "Sauyin jihar Tibet". Ya ce, idan ya sami lafiya, zai ci gaba da rubuta wani littafi. Yayin da yake dakin asibiti, ya bayyana fatansa ga shugaban aikinsa da dalibai cewa, zai kai ziyara a jihar Tibet ta jirgin kasa."

A shekarar 2005, Israel Epstein ya je gidan gaskiya a kasar Sin. A cikin duk rayuwarsa, ya kai ziyara a jihar Tibet har sau 4. Ko da yake bai cimma burinsa ba na kai ziyara a jihar Tibet ta jirgin kasa, amma a matsayin manzon kasar Sin mai sada zumunta, ya riga ya kammala aikinsa na gabatar da kasar Sin ga kasashen duniya, kuma ya ga babbar sauyawar da kasar Sin ta samu. Yanzu jama'ar Sin suna ta tunawa da shi kwarai da gaske.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China