in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kalmomin Sinanci
2009-12-10 15:21:28 cri
Jama'a masu karatu, muna fatan kome na gudana yadda ya kamata a gare ku. A wannan kashi kuma, ba shakka za mu fara karanta sakwanninku kamar yadda muka yi a da. Da farko, ga wani sako daga mai sauraronmu a kullum malam Abdou Nenne daga kasar Nijeriya, inda ya bayyana cewa, "Abin da nake nufi a nan shi ne ku karanta mini da sakon a cikin shirye-shiryenku. na gode muku. Kuma ina fatan ba za ku gaji da yawan sakonnin da nake damunku da su ba."

To, mun gode, malam Abdou Nenne, a tarayyar Nijeriya. A hakika dai, kome ba mu gaji da shi ba. A maimakon hakan, duk ma'aikatanmu muna farin ciki kwarai sabo da yawan sakwanni masu ma'ana da kuka aiko mana. Ko kun san cewa, wadannan sakwanni sun ba mu dama da kuma jaruntaka wajen ci gaba da gabatar muku da shirye-shirye masu kyau. Da fatan za ku kara aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayinku da kuma ba da shawarwari. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.

To, sakon malam Abdou Nene ke nan. A tsakiyar watan jiya, shugaban Amurka Barack Obama ya kai ziyara a kasar Sin da sauran wasu kasashen Asiya. Game da lamarin kuma, mun riga mun gabatar muku a cikin shirinmu a baya. Masu sauraronmu da dama sun aiko da wasiku domin bayyana ra'ayinsu. Malam Issa Musa daga Bertoua a Cameroun ya bayyana cewa, "Ina yiwa mutanen kasar Sin murna da Barack Obama ya je lafiya ya kuma koma lafiya." Yayin da malam Abba Tahir daga jami'ar Bayero dake Kano, tarayyar Nigeria ya bayyana cewa, "Alal hakika ziyarar shugaba Obama zuwa Asia tana muhimmanci sosai." Kuma malam Nagarba Abdoul Rasmane daga birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar Burkina Faso ya rubuto mana wasika cewa, "Barack Obama shugaba ne mai neman zaman lafiya. Ziyararsa a kasar Sin tana tabbatar da cewa, lalle a yanzu kasar Sin wata kasa ce dake samun babban ci gaba, kuma tattalin arzikinta yana bunkasa yadda ya kamata. A sabili da haka, shi shugaba Obama yana neman hadin gwiwa da kasar Sin."

To, mun gode duk wadanda suka aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayinsu kan ziyarar Barack Obama a kasar Sin. Wasu sun nuna goyon baya kan lamarin, yayin da wasu suka nuna rashin amincewa. Duk da haka kuwa, mun gano cewa, lalle Sin tana bunkasa yadda ya kamata, kuma tana fatan sada zumunta da hadin gwiwa da bangarori daban daban na duniya baki daya.

To, a kwanan baya, mun samu wani sako daga malam Ahmed Danlami daga Borno, tarayyar Nijeriya, inda ya bayyana mana cewa, "Ina sha'awar Sinanci sosai. Kuma ina koyonsa bisa iyakacin kokari. Don Allah ko za ku gabatar mini da wani bayani kan kalmomin Sinanci?" To, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya.

Kasar Sin tana kunshe da kabilu 56. A sabili da haka, tana da harsuna sama da 80 tare da ire-iren kalmomi kimanin 30.

A cikin kasar Sin har ma a duk duniya, mafi yawan mutane suna yin amfani da Sinanci, kuma yana daya daga cikin harsuna 6 da MDD take yin amfani da su. A kasar Sin, 'yan kabilar Han su kan yi magana da Sinanci, wadanda yawansu ya kai kimanin kashi 92 cikin kashi dari, hatta ma a wasu kananan kabilu na kasar. Ban da kabilar Hui da ta Man, sauran kananan kabilu suna amfani da Sinanci baki daya. Duk da haka kuwa, wadannan kananan kabilu 53 suna da harsunan kansu. A wasu kananan kabilu, mutane su kan yi amfani da harsuna biyu.

Ana yin amfani da Putonghua, wato daidaitaccen Sinanci a duk fadin kasar Sin.

Sinanci yana da dogon tarihi na tsawon shekaru 6000. Kalmomin Sinanci da ake yin amfani da su a yanzu sun samu asali na kalmomin zamanin da. Ban da kabilar Han, wasu kananan kabilun Sin suna amfani da kalmomin Sinanci. Tun bayan shekaru 50 na karnin da ya gabata, an fara tsara da saukaka kalmomin Sinanci, kuma an gabatar da "Shirin saukaka kalmomin Sinanci" da "Takardar kalmomin Sinanci da a kan yi amfani da su" da dai makamantansu. A ran 31 ga watan Oktoba na shekarar 2000, an fito da doka mai kula da kalmomi na daidaitaccen harshen jamhuriyyar jama'ar Sin", wadda ta dauki daidaitattun kalmomin harshen Han a matsayin kalmomin gwamnati.

Kafin kafa sabuwar kasar Sin, kananan kabilun Sin 21 suna da kalmomin kansu. Bayan kafuwarta kuma, gwamnatin ta tsara shirin kalmomi ga kabilar Zhuang da Buyi da Yi da Miao da Hani da Naxi da Dong da dai sauransu.

Bisa ka'idar "dukkan kabilun Sin suna cikin adalci", gwamnatin Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar harsuna cikin adalci, kuma tana kiyaye nau'o'insu. Kundin tsarin mulkin kasar Sin da dokar kula da harkokin yankunan Sin da dokar ilmi ta kasar Sin da sauransu sun tabbatar da matsayin wadannan harsuna cikin adalci, kuma sun hana nuna bambanci ga harsuna iri daban daban ta kowace hanya. Kowace kabila tana da 'yancin yin amfani da kuma raya harshenta. kasar Sin tana sa kaimi ga kabilu da su koyi harsuna da kalmomi daga juna, kuma tana gabatar da Putonghua da daidaitattun kalmomin harshen Han yadda ya kamata. Sin tana aiwatar da dukkan wadannan muhimman manufofin harsuna a yunkurin tabbatar da bunkasuwar harsuna na kabilu daban daban cikin lumana. Hakan zai ba da babban taimako ga kiyaye dinkuwar kasar Sin da hada kan kabilu daban daban da sa kaimi ga bunkasuwar zamantakewar al'umma da tattalin arziki da al'adu na kasar Sin baki daya.

To, jama'a masu karatu, yanzu bayani ke nan kan tambayar malam Ahmed Danlami daga Borno, tarayyar Nijeriya, da fatan ka ji ka gamsu da shi.

Bayan haka, kwanan baya, mun samu sakwanni da dama daga wajen masu sauraronmu, ciki har da wani daga malam Muhamed Dawaisu daga Bauchi, tarayyar Nijeriya, da malam Shuaibu Muhammed Rijiyar maikabi, daga Kebbi, tarayyar Nijeriya da dai sauransu, wadanda ba mu iya karanta sakwanninsu duka ba, sabo da karancin lokaci. Don haka muna farin ciki, da fatan za ku ci gaba da sauraron tashar CRI. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China