in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin ta shirya liyafa domin murnar babbar sallah
2009-11-28 20:57:50 cri
Ranar 28 ga wata rana ce ta babbar sallah ga mutane masu bin addinin musulunci. Sabo da haka, a wannan rana da dare, kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin ta shirya liyafa a nan birnin Beijing domin murnar wannan babbar sallah. Mr. Hui Liangyu, mataimakin firayin ministan kasar Sin ya halarci wannan liyafa.

Babban imam Chen Guangyuan, shugaban kungiyar addinin musulunci ta kasar Sin ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, a bana, kungiyarsa ta taimaki musulman kasar Sin dubu 12 da dari 7 domin yin aikin hajji a Mecca. Haka kuma, gwamnatin kasar Sin ta shisshirya sosai wajen tsaro da kuma tabbatar da lafiyar musulmai wadanda suka yi aikin hajji a Mecca.

Musulmai fiye da dari 3, ciki har da jakadun kasashe masu bin addinin musulunci da ke nan kasar Sin da baki masana musulmai da suke aiki a nan Beijing da wakilai musulmai na bangarori daban daban sun halarci wannan liyafa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China