in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauyin zaman rayuwar masunta a tsibiran Xisha na Sin
2009-11-12 21:19:03 cri

Tsibiran Xisha suna yankin kudancin teku na Sin, wadanda suke da tazarar kilomita 330 daga kudu maso gabashin lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, yana kunshe da tsibirai da yawa, tare da albarkatun kifaye. Tun zamanin da, masunta suna ta yin aikinsu a wannan yankin na teku. Duk da haka kuwa, tsibiran Xisha suna nisa da babban yankin Sin, da kyar ake iya yin sufuri. A sabili da haka, zaman rayuwar masunta a tsibiran yana cikin mawuyacin hali. Amma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, bisa kulawa da kuma goyon bayan gwamnatin wurin, zaman rayuwarsu na sauyawa a yau da kullum. Yanzu bari mu kai ziyara mu ga yadda suke zaman rayuwa.

Bayan kwashe awoyi 15 a cikin jirgin ruwa daga birnin Wenchang na lardin Hainan, mun isa tsibirin Yongxing, wanda tsibiri ne mafi girma a cikin tsibiran Xisha na Sin. Fadinsa ya kai muraba'in kilomita 2, wanda ya yi kama da wani lu'u mai launin kore a ruwan teku mai launin shudi.

Bayan isarmu, masunci Fu Zaichou da matarsa suka fito daga gari suna maraba da zuwanmu. Fu Zaichou dai dogo ne. Yayin da ya yi magana kan aikinsa na su, ya yi farin ciki, inda ya bayyana cewa,

"Ana samun sauki wajen kama kifaye a wannan yanki. Mu kan fita da safe domin aiki, kuma mu koma gida da dare. Kowane lokaci, yawan kifaye da muka kama ko kuma mu kan saya daga wasu masunta a sauran tsibirai ya kai sama da kilomita dari."

Bisa gabatarwar da Fu Zaichou ya yi, a lokacin da, kowane iyali ya kan samu kudin shiga yuan dubu 20 zuwa dubu 30 ne kawai a kowace shekara sabo da mawuyacin halin gudanar da aiki. Amma yanzu, amfani da kayayyakin su na zamani da karuwar bukatar kasuwancin kifaye sun taimaka wajen kara musu kudin shigarsu zuwa yuan dubu 30 ga kowane mutum a kowace shekara. Karuwar kudin shiga ta kawowa Fu Zaichou da iyalinsa alheri. Amma babbar sauyawar da tsibirin Yongxing ya yi ta fi faranta zukatansu, wadda ta saukaka zaman rayuwarsu a kai a kai.

Da farko, an kyautata matsalar karancin wutar lantarki a tsibirin. A da, ana yin amfani ne da kananan na'urorin samar da wutar lantarki, wadanda suka da karfin biyan bukatun jama'a kadan kawai. Daga bisani, zaman rayuwar jama'a ya samu kyautatuwa, yawan wutar lantarki da ake bukata na ta karuwa. A sabili da haka, a shekarar 2007, kwamitin kula da aikin tsibiran Xisha, Nansha da Zhongsha ya kafa na'urori biyu na samar da wutar lantarki masu karfin kilowatt 300, wadanda suka taimaka wajen sassauta wannan matsala sosai. Bayan haka, ana share fagen kafa kayayyakin samar da wutar lantarki ta amfani da karfin iska da hasken rana, a yunkurin kara saukaka matsalar karancin wutar lantarki tare da kiyaye muhalli.

Dadin dadawa, mazaunan tsibirin su kan yi fama da batun karancin ruwan sha. A kan yi jigilar ruwan sha daga tsibirin Hainan na Sin. Garin Nan da masunci Fu Zaichou yake zaune, yana da mazauna sama da 30, wadanda su kan yi amfani da ruwan sha kimanin ton 50 ne kawai a rabin shekara. Fu Zaichou ya gabatar mana halin yin amfani da ruwa yana mai cewa,

"Kowa ya san amfani da darajar ruwan sha, shi ya sa ake yin tsimi sosai. Idan ana wanke ganyaye ko sauran abubuwa, a kan wanke su da ruwan teku tukuna, daga baya kuma a yi amfani da ruwan sha."

Game da wannan lamari, kwamitin ya fito da shirin tabbatar da samun bunkasuwa a nan gaba. Sakamakon daidaita matsalar karancin wutar lantarki da aka yi a tsibirin, akwai yiwuwar a tabbatar da wutar lantarki da za a yi amfani da ita wajen tsabtace ruwan teku. Mataimakin darektan kwamitin Tan Xiankun ya bayyana cewa,

"An riga an gabatar da shirin tsabtace ruwan teku, kuma farashinsa yana dacewa da halin da ake ciki. Dadin dadawa, akwai aikin kyautata ruwan dake gurbata muhalli. Bayan haka, za a iya yin amfani da wannan ruwa domin wanka ko kuma wanke tufafi da sauransu. A sakamakon haka, mazaunan tsibirin za su iya yin amfani da ruwa mai tsabta ba ma kawai a fannin ruwan sha ba, har ma a fannin zaman rayuwa."

Bayan haka kuma, kafa gidan aika wasiku, da kaddamar da siginar salula sun saukaka mu'amala tsakanin mazaunan tsibirin da sauran jama'a. Kafin wannan kuma, mazaunan tsibirin su kan yi mu'amala da sauran mutane da wayar tarho ta gidan aika wasiku, wadda take da tsada sosai. Duk da haka, a kan samu mutane masu dimbin yawa domin buga wayar tarho. Bisa kokarin gwamnati, kamfanin sadarwa na China Mobile da na China Unicom sun kaddamar da ayyuka a tsibirin, a sabili da haka, mazaunan sun sami sauki sosai wajen buga waya.

Bugu da kari kuma, a ran 30 ga watan Yuli na shekarar 2007, an kaddamar da aikin yanar gizo ta internet a tsibirin, tare da wata cibiyar internet, wadda take kunshe da na'urori masu kwakwalwa guda 30. Ji Haiwu, wani masunci mai shekaru 20 a duniya, yana hira da abokai ta yanar gizo ta internet a maimakon aikin su, sabo da yanayi maras kyau. Yayin da yake magana kan lamarin cikin farin ciki ya bayyana cewa,

"Idan ina son ganin abokaina, sai na yi amfani da na'ura mai kwakwalwa ta yanar gizo. Yana da sauki sosai kuma da araha bisa bi hanyar buga wayar tarho."

Ban da wadannan kuma, an riga an kafa asibitoci da bankuna da kantuna a tsibirin, tare da dakin kwallon tebur, wanda masunta suna iya yin amfani da shi ba tare da biyan kudi ba. Ana zama a tsibirin kamar yadda ake yi a babban yanki.

Tare da kafuwar manyan ayyuka a tsibirin, an ba da tabbaci ga zaman rayuwar masunta. A sabili da haka, suna iya aiki yadda ya kamata ba tare da nuna damuwa ba, kuma suna da buri ga zaman rayuwa a nan gaba.

Yayin da yake tabo maganar shiri a bana, masunci Fu Zaichou ya nuna wani dakin dake gaban gidansu, inda ya dasa na'urori 7 masu sanyaya kayayyaki dake cike da albarkatun teku, ya bayyana cewa, wadannan kifaye za su biya bukatun mazaunan tsibirin na tsawon kwanaki 7 ne kawai idan ba a iya kama kifaye ba sabo da yanayi maras kyau. Amma yana share fagen kara fadin wannan daki a yunkurin tinkarar wannan matsala. Ga abin da ya ce,

"Kafin wannan, sabo da karancin wutar lantarki, ba a iya yin amfani da na'urori masu sanyaya kayayyaki ba. Amma yanzu muna da isasshiyyar wutar lantarki, wadda za ta kara karfin sanyaya kayayyaki. Nan ba da dadewa ba, sabon dakin zai kafu, wanda zai ninka sau da dama bisa na yanzu. A sakamakon haka, za a iya kara mikewa wajen kama kifaye a ajiye a ciki."

Matar Fu Zaichou ta yi murmushi ta bayyana fatanta na gaba, ga abin da ta ce,

"Ina fatan zaman rayuwar mazaunan tsibiran Xisha zai kara samun kyautatuwa, tare da samun damar kama kifaye masu dimbin yawa. Za mu kara kokari a yunkurin biyan bukatun jama'ar tsibiran Xisha na cin kifaye."(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China