in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani dan kabilar Hui da zaman rayuwarsa na tsawon shekaru 60
2009-11-08 19:57:09 cri

Kabilar Hui wata kabila ce da ake iya samun musulmai mafi yawa a cikin kananan kabilun kasar Sin. A ran 18 ga watan Disamba na shekara ta 1949, an haifi Wu Jinzeng a cikin wani gidan musulmi 'yan kabilar Hui a birnin Beijing. A wancan lokaci, an kafa sabuwar kasar Sin ba da jimawa ba, ko da yake dukkan abubuwa suna jiran samun farfadowa, amma an kawo wa jama'ar Sin fatan alheri na jin dadin zaman rayuwa. Wu Jinzeng ya bayyana cewa, tun lokacin kuruciyarsa, mahaifinsa ya gaya masa cewa, tabbas ne a yi kokarin karatu. Sabo da an kafa sabuwar kasar Sin ba da jimawa ba, shi ya sa ba za a iya jin dadin zaman rayuwa ba sai dai an yi matukar kokari. Kuma ya ce,

"Lokacin da nake makarantar firamare, mahaifina ya gaya mini cewa, tabbas ne a yi kokari a fannin karatu, da kuma lura da zamanmu na yanzu da ba za a same shi ba cikin sauki. A wancan lokaci, kasarmu ta fara samun farfadowa, ko da yaushe mahaifina ya kan gaya mini cewa, ba za a iya bayar da gudummowa ga bunkasuwar kasarmu ba sai an samu ilmi sosai, ta yadda zamanmu zai iya samun kyautatuwa."

Tunawa da kalaman da mahaifinsa ya yi, Wu Jinzeng ya gama karatunsa a makaranta, kuma ya ganar wa idonsa yadda sabuwar kasar Sin ke fama da talauci a karkashin jagoranci JKS, dukkan wadannan abubuwa sun karfafa zuciyar Wu Jinzeng wajen bayar da gudummowa ga bunkasuwar kasar. Don haka yayin da ake kira da a je yankunan karkara da yankunan da ke da wuyar zuwa don samar da taimako ga bunkasuwarsu, a shekara ta 1969, Wu Jinzeng mai shekaru 18 da haihuwa ya je Yan'an na lardin Shanxi da ke arewa maso yammacin kasar Sin, da kuma fara yin ayyukan gona.

Wu Jinzeng da ya girma a birnin Beijing ya gamu da dimbin wahalhalu bayan da ya isa yankin karkara ba da jimawa ba, amma sharuda marasa kyau da kuma dimbin ayyuka ba su sage masa gwiwa ba, ya gaya mana cewa, a wancan lokaci, yana da aniya daya kawai, wato raya kasa bisa iyakacin kokarinsa. Kuma ya ce,

"A wancan lokaci, ina da karfin zuciya sosai wajen zuwa yankunan karkara domin samun jarrabawa. Sharadin wurin ba ya da kyau sam, wanda ba za a iya kwatanta shi da na Beijing ba, amma ban taba tsoron shan wahala ko jin gajiya ba, kamar ina da karfin da bai iya karewa ba. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ina jin alhafari da na iya bayar da gudummowa ga bunkasuwar kasarmu."

Sakamakon fice da ya yi, bayan shekara guda, an gabatar da Wu Jinzeng zuwa wata masana'antar da ake ginawa domin zama wani ma'aikacin yin molin kayayyaki ne. Ya gaya mana cewa, a wancan lokaci, masana'antar da ake ginawa tana kan wani wuri maras amfani, shi ya sa aka kaddamar da aiki daga farko. Ko da yake dakin da suke kwana yana da sauki, kuma aikinsu ya yi matukar yawa, amma ba su ji tsoro ba. Wu Jinzeng ya bayyana cewa,

"A wancan lokaci, muna da karfin zuciya sosai, har ma ba mu lura da abinci ba. Ko da yaushe mu kan yi tafiya muna cin abinci, yayin da muke isa masana'anta, muna ci gaba da aiki. A lokacin aiki kuma, har ma mu kan manta da zuwa bayan gida."

Bayan da aka kammala gina sabbin dakunan masana'antar, kuma injuna suka fara aiki, Wu Jinzeng da abokan aikinsa sun yi alhafari kwarai. Bayan da masana'antar ta fara aikin samarwa, sharadin aiki da kuma na zaman rayuwa dukkansu suna samun kyautatuwa. Sakamakon hazaka da kuma kokarinsa, kwarewar aikin Wu Jinzeng tana ta kyautatuwa, amma bai gamsu da wannan ba. Haka kuma a wannan lokaci, wato a shekara ta 1978, kasar Sin ta fara bude kofa ga waje da kuma yin kwaskwarima a gida, masana'antar Mr. Wu ta samu bunkasuwa sosai. Mr. Wu yana ganin cewa, ilminsa a fannin fasaha bai isa ba, don haka ya tsai da kudurin ci gaba da karatu.

Haka kuma a wannan shekara, an haifi diyarsa Wu Jing. Haihuwar Wu Jing ta faranta ran Wu Jinzeng da matarsa sosai, ko da yaushe a kan iya jin muryar murna a gidansa. Amma domin nuna kulawa ga diyarsa da kyau da kuma kara karatu, Mr. Wu da matarsa sun tsai da kudurin kebe sulusin yawan albashinsu a ko wane wata domin yin hayar wata mai reno don ta dinga kulawa da diyarsu. Mr. Wu ya bayyana cewa,

"Domin ci gaba da karatu da kuma kaucewa yin illa ga aiki, ni da matata mun tsai da kudurin yin hayar wata mai reno. A wancan lokaci, kudin na da yawa sosai, amma mun yi haka ne domin kulawa da diyata tare da daina dakatar da aiki da karatu."

Fasahar da Wu Jinzeng ya samu ta daga wani sabon mataki sakamakon kokari karatunsa, kuma ya zama wata kusa a ma'aikatar. Dukkan wadannan abubuwa sun yi tasiri sosai ga diyarsa. Tun lokacin kuruciyar Wu Jing, mahaifinta ya zama abin koyi na farko a zaman rayuwarta. Wu Jing ta gaya mana cewa,

"sakamakon kokarin mahaifina a fannin aiki, ni ma na samu wata kyakkyawar dabi'a wajen kokarin karatu. Kuma bayan da na fara aiki, na ci gaba da nuna himma da kwazo ga aikina. Ina fatan zan iya bayar da gudummowata ga bunkasuwar kasarmu bisa kokarina kamar yadda mahaifina ke yi."

A shekara ta 1986, Wu Jinzeng ya dawo birnin Beijing daga lardin Shanxi, da kuma gudanar da aikin kera kayayyakin motoci a cikin masana'antar samar da injuna masu amfani da man dizal. A farkon dawowarsa birnin Beijing, sabo da Wu Jinzeng wani dan kabilar Hui ne, shi ya sa masana'antar ta ba shi wani dakin kwana daga cikin dakunan kwana kalilan.

Yanzu Wu Jinzeng ya riga ya yi ritaya, yanzu ban da kulawa da jikarsa, shi ma ya kan shiga harkoki iri daban daban. Wu Jinzeng ya bayyana cewa,

"Yanzu na kan je masallaci don sauraron bayanan Alkur'ani da limamai suke yi da kuma yin salla. A wasu lokuta ma na kan yi raye-raye da zane-zane, lallai zaman rayuwar tsoffi yana da kyau kwarai da gaske yanzu."

Yayin da yake tunawa da zaman rayuwarsa, Wu Jinzeng ya gaya mana cewa, yana yin alfahari da ya iya girma da kuma samun ci gaba tare da kasar Sin bisa kokarinsa. Kuma ya kara da cewa,

"A matsayina na wani mutumin da ke da shekaru iri daya tare da kasar mahaifata, ina alfahari sosai. A cikin shekaru 60 da suka gabata, zamanmu yana ta samun kyautatuwa a ko wace rana. Kuma kasar Sin ta samu nasarori a fannoni daban daban, don haka na ji farin ciki sosai. A ganina, kasarmu za ta samu wata kyakkyawar makoma sakamakon samun bunkasuwa a cikin shekarun nan da suka gabata."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China