Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
• Zuwa ga masu karatu  [ Tambayoyi guda 6 ]
Bayan haka muna sanar da ku cewa,daga ran 28 ga watan Nuwamba na shekarar 2006,mun soma wata gasar kacici-kacici,dangane da "Garin panda---jihar Sichuan".Kuma za mu gama gasar a ran 15 ga watan Aflilu na shekarar 2007.Kuna iya samun amsa a cikin shirinmu na `Yawon shakatawa a Kasar Sin` wanda mu kan gabatar muku a kowace ranar Talata.Kamar yadda muka yi muku alkawari,za mu ba da kyaututtuka ga wadanda suka amsa tambayoyin daidai.
• Gidan Panda: gandun daji na Wolong na lardin Sichuan
A cikin shirin musamman namu na karshe, za mu tabo magana dangane da dabbar Panda, wata alama ce ta lardin Sichuan. Za mu kai ziyara ga gandun daji na Wolong. Kafin mu soma shirinmu na yau, sai tambayoyi 2 da muka yi muku, da farko a wane lardi ne garin Panda yake? Na biyu kuma Panda nawa ne suke zama a cikin kunkurmin daji na gandun daji na Wolong?
• Gasar kacici-kacici: Babban dutse na Qingchengshan da madatsar ruwa ta Dujiangyan
A cikin shirinmu na yau, za mu ziyarci babban dutse na Qingchengshan da kuma madatsar ruwa ta Dujiangyan, wadanda ke cikin takardar sunayen wuraren tarihi na al'adu na duniya. Kafin mu soma shirinmu na yau, gi tambayoyi 2 da muka shirya muku, da farko ko an mayar da babban dutse na Qingchengshan tamkar mafari na addinin Taoism? Na biyu kuma, yaushe ne aka gina madatsar ruwa ta Dujiangyan?
• Gasar kacici-kacici: Fahimtar addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan
Jama'a masu karatu, muna muku godiya da sauraren shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Garin Panda, lardin Scihuan'. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga manyan duwatsun Emeishan da Leshan. Kafin mu soma shirinmu na yau, bari mu yi muku tambayoyi 2 tukuna. Da farko ko babban dutse na Emeishan na daya daga cikin wurare masu tsarki na addinin Buddha na kasar Sin ko a'a? Na biyu, mutum-mutumin babban Buddha na Leshan mutum-mutumi ne mafi girma na Buddha a duk duniya, tsayinsa ya kai mita nawa ne?
• Wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki
A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga wani wurin tarihi wai shi Sanxingdui. Kafin mu soma shirinmu na yau, bari mu yi muku tambayoyi 2 tukuna. Da farko shekaru nawa ne da wayin kai na wurin tarihi na Sanxingdui ya yi suna sosai? Na biyu kuma, a cikin abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin wurin tarihi na Sanxingdui, mene ne ya fi nuna nagartacciyar fasahar zamanin da, abubuwan da aka yi da lu'ulu'u ko kuma wadanda aka yi da tagulla?
• Ziyarar Aljannar da ke duniyarmu---kai ziyara ga kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong
A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga sansannun kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong da ke yammacin lardin Sichuan, wadanda Sinawa su kan mayar da su tamkar Aljannar da ke duniyarmu. Da farko dai, za mu gabatar muku da tambayoyi 2, su ne, ko asalin sunan kwarin Jiuzhaigou yana da nasaba da kauyuka 9 na kabilar Zang da ke cikin wannan kwari ko a'a. Na biyu, ko an tanadi kwarin Jiuzhaigou da wurin shakatawa na Huanglong a kan takardar sunayen wuraren tarihi na halitta na duniya ko a'a? Jama'a masu sauraro, sai ku karkade kunnuwanku don jin abubuwan da muka shirya, ta haka za ku amsa tambayoyin da muka yi muku.