Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-19 21:44:01    
Zuwa ga masu karatu  [ Tambayoyi guda 6 ]

cri

Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri da kuma fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

Bayan haka muna sanar da ku cewa,daga ran 28 ga watan Nuwamba na shekarar 2006,mun soma wata gasar kacici-kacici,dangane da "Garin panda---jihar Sichuan".Kuma za mu gama gasar a ran 15 ga watan Aflilu na shekarar 2007.Kuna iya samun amsa a cikin shirinmu na `Yawon shakatawa a Kasar Sin` wanda mu kan gabatar muku a kowace ranar Talata.Kamar yadda muka yi muku alkawari,za mu ba da kyaututtuka ga wadanda suka amsa tambayoyin daidai.

To, ga tambayoyi guda 6:

1. A wace jiha garin panda yake?

A) Jihar Sichuan B) Jihar Guizhou C) Jihar Guangxi

2. Kimanin panda nawa ne a cikin kungurmin daji na Sichuan?

A) Fiye da 50 B) Fiye da 100 C) Fiye da 150

3. Kauyukan kabilar Tibet nawa ne a ni`imtaccen yankin `Jiuzhaigou`?

A) Guda 7 B) Guda 8 C) Guda 9

4. A cikin abubuwan tarihi na `Sanxingdui`,mene ne ya fi nuna fasahar zamanin da?

A) Abubuwan da ake yi da tagulla B) Abubuwan da ake yi da zinariya

C) Abubuwan da ake yi da azurfa

5) Tsayin kayan sassaka na mutum mutumin na Babban Buddha `Leshan` ya kai mita nawa?

A) Mita 50 B) Mita 70 C) Mita 90

6. Yaushe ne aka gina madatsa ruwa wato `Dujiangyan` ?

A) Kafin shekaru 1000 B) Kafin shekaru 1500 C) Kafin shekaru 2000

To, mai sauraro, bayan ka ba da amsa, sai ka aiko mana da wasika ta hanyar yin amfani da wannan ambulan da muka biya kudin kan sarkinsa, wato ba tare da kun biya ko kwabo daya ba.

Haza Wassalam

Daga Sashen Hausa Na Rediyon kasar Sin