Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-12 15:56:21    
Fahimtar addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan

cri

Jama'a masu karatu, muna muku godiya da sauraren shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Garin Panda, lardin Scihuan'. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga manyan duwatsun Emeishan da Leshan. Kafin mu soma shirinmu na yau, bari mu yi muku tambayoyi 2 tukuna. Da farko ko babban dutse na Emeishan na daya daga cikin wurare masu tsarki na addinin Buddha na kasar Sin ko a'a? Na biyu, mutum-mutumin babban Buddha na Leshan mutum-mutumi ne mafi girma na Buddha a duk duniya, tsayinsa ya kai mita nawa ne?

Babban dutse na Emeishan ya zama na farko a duk kasar Sin tun daga can can can da. A cikin dukan sansannun manyan duwatsu na kasar Sin, babban dutse na Emeishan mai tsayin mita fiye da dubu 3 yana kan gaba a fannin tsayi. Tsire-tsire iri daban daban suna zama lami lafiya saboda zafin nan ya sha bambansosai a tsakanin kololuwar wannan babban dutse da kuma gindinsa. Yawan ire-iren tsire-tsiren da aka samu a babban dutse na Emeishan ya zarce dubu 5, wanda ya yi daidai da jimlar ire-iren tsire-tsiren da ke zama a dukan kasashen Turai, daga cikinsu kuma akwai wasu ire-irensu da ba safai a kan gan su ba a duniya. In an sa kafa a kan babban dutsen, sai idanunsa cike suke da kwarran ganyaye saboda tsoffin dogayen itatuwa suna kan gefunan hanyoyi.

A sakamakon sauye-sauyen yanayi da bambancin tsare-tsaren babban dutse, babban dutse na Emeishan ya fi kyan gani.

Halin musamman da babban dutse na Emeishan ke nunawa yana dangane da al'adun addinin Buddha, wanda ya aza harsashi a nan sosai. A cikin karni na 1, an yada addinin Buddha daga kasar Indiya zuwa babban dutse na Emeishan, an kuma gina gidan ibada na addinin Buddha na farko na kasar Sin a nan. Saboda kafuwar sauran gidajen ibada na addinin Buddha da ke kewayensa, babban dutse na Emeishan ya zama daya daga cikin wurare masu tsarki na kasar Sin a fannin ya da addinin Buddha sannu a hankali. Mutane suna aikin hajji a nan.


1  2  3