Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-05 18:41:36    
Wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki

cri

Jama'a masu sauraro, muna muku godiya da sauraren shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Garin Panda, lardin Sihuan'. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga wani wurin tarihi wai shi Sanxingdui. Kafin mu soma shirinmu na yau, bari mu yi muku tambayoyi 2 tukuna. Da farko shekaru nawa ne da wayin kai na wurin tarihi na Sanxingdui ya yi suna sosai? Na biyu kuma, a cikin abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin wurin tarihi na Sanxingdui, mene ne ya fi nuna nagartacciyar fasahar zamanin da, abubuwan da aka yi da lu'ulu'u ko kuma wadanda aka yi da tagulla?

Abubuwan da wani bakauye na kauyen Sanxing ya gano a lokacin da yake aiki a gona da kuma hakan kayayyakin gargajiya da nazarin da aka yi shekaru gomai ana yi sun tabbatar da cewa, yau da shekaru dubu 5 zuwa dubu 3 da suka wuce, kauyen Sangxing babban birnin ne na karamar kasar Shu ta zamanin da, wayin kansa ya taba yin suna har shekaru misalin dubu 2 da suka wuce. Saboda irin wannan muhimmiyar ganowa, an kyautata tsare-tsaren tarihin wayin kai na kasar Sin, ya kuma nuna cewa, wayin kai na Kogin Yangtze da wurin tarihi na Sanxingdui yake wakilta ya yi daidai da na Rawayan Kogi, dukansu suna cikin tsarin wayin kai na kasar Sin.

Kauyen Sanxing yana cikin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin. A sakamakon babban gano da aka samu yau da shekaru 75 da suka shige, an gina dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya mai suna Sanxingdui a wurin tarihi na Sanxingdu yau da shekaru misalin 10 da suka wuce.

Mai ba da karin haske madam Qiu Xueqing na wannan dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya ta bayyana cewa, gano wannan wurin tarihi na wayin kai yana da muhimmanci sosai. Ta ce, (murya ta 1, Qiu Xueqing)

'An gano wannan wurin tarihi ne a kan layin da ya zagaye duniya a arewa mai misali digiri 30, ban da shi kuma, akwai babban dutse na Everest da wayin kai na Maya da babban tsibiri na Bermuda a kan wannan layi. Dukansu suna da ban mamaki. Wurin tarihi na Sanxingdui wani birni ne na zamanin da inda har zuwa yanzu aka fi samun kayayyakin gargajiya, sa'an nan kuma, tarihinsa ya fi tsayi, kuma yana kunshe da abubuwan al'adu iri daban daban a dukan yankin kudu maso yammacin kasar Sin.'

Masu ilmin nazarin kayayyakin gargajiya sun gano cewa, yau da shekaru misalin dubu 3 da suka wuce, an yi watsi da wannan cikakken birni ba zato ba tsammani, shi ya sa aka sa aya ga nagartaccen wayin kai na Sanxingdui ba zato ba tsammani. Akwai jita-jita da yawa kan anihin dalilin da ya sa aka yi watsi da wannan birni mai shekaru misalin dubu 2, amma har zuwa yanzu dai yana daure kan mutane sosai, saboda babu rubutu ta fuskar tarihi.

Kayayyakin gargajiya da aka samu a wurin tarihi na Sanxingdui sun fi ba mutane mamaki. Madam Qiu Xueqing ta gaya mana cewa, abubuwan da suka fi jawo hankali su ne kayayyakin da aka yi da tagulla. Fuskokin wasu mutanen da aka sassaka a kan mutum-mutumin tagulla sun sha bamban da na mutanen kasashen Asiya kwarai, suna da manyan idanu da kuma hanci mai tsayi.

Kayayyakin tagulla daban da suka fi shahara su ne manyan itatuwa na tagulla, an mayar da su tamkar abin al'ajabi na duniya. Tsayinsu yanzu ya kai mita misalin 3.6. Mutanen Sin na da suna ganin cewa, itace na siffantar sararin samaniya gaba daya, taurari da wata da rana da duniya dukansu 'ya'ya ne da ke kan itacen. Wadannan manya itatuwa marasa biyu ne a duk duniya a fannin siffofinsu da kuma fasahar kera.

A gaskiya kuma, ban da nagartacciyar fasaha, wadannan itatuwan tagulla sun bayyana ra'ayin da mutanen kasar Sin suke tsayawa a kai a kan duniya a zamanin da.

Ma iya cewa, kayayyakin tagulla sun fi wakiltar kayayyakin gargajiya da aka samu a wurin tarihi na Sanxingdui. Sun fi nuna nagartacciyar fasahar zamanin da.

An taba nuna kayayyakin gargajiya na Sanxingdui a kasashen waje, kayayyakin gargajiya masu ban mamaki da kuma tsohon wayin kai mai daure kai na wurin tarihi na Sanxingdui sun jawo hankulan masu yawon shakatawa na kasashen waje kwarai da gaske. Madam Sirkka Korela, 'yar kasar Finland, ta yi mamaki da wurin tarihi na Sanxingdui kwarai. Ta ce, 'An ajiye kayayyakin gargajiya ta hanya mai cikakken bambanci. Abubuwan da suka fi jawo hankalina su ne wadannan kayayyakin gargajiya, musamman ma abubuwan rufe fuska masu ban mamaki, haka kuma wadannan itatuwa da tsuntsaye na tagulla.'

Masu yawon shakatawa su kan sami ra'ayoyinsu daban daban game da wannan wurin tarihi mai ban mamaki, bayan da suka ziyarci dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya mai yawan kayayyakin gargajiya.

To, kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyi 2 da muka yi muku. Da farko shekaru nawa ne da wayin kai na wurin tarihi na Sanxingdui ya yi suna sosai? Na biyu kuma, a cikin abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin wurin tarihi na Sanxingdui, mene ne ya fi nuna nagartacciyar fasahar zamanin da, abubuwan da aka yi da lu'ulu'u ko kuma wadanda aka yi da tagulla?