Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-28 17:28:39    
Ziyarar Aljannar da ke duniyarmu---kai ziyara ga kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga sansannun kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong da ke yammacin lardin Sichuan, wadanda Sinawa su kan mayar da su tamkar Aljannar da ke duniyarmu. Da farko dai, za mu gabatar muku da tambayoyi 2, su ne, ko asalin sunan kwarin Jiuzhaigou yana da nasaba da kauyuka 9 na kabilar Zang da ke cikin wannan kwari ko a'a. Na biyu, ko an tanadi kwarin Jiuzhaigou da wurin shakatawa na Huanglong a kan takardar sunayen wuraren tarihi na halitta na duniya ko a'a? Jama'a masu sauraro, sai ku karkade kunnuwanku don jin abubuwan da muka shirya, ta haka za ku amsa tambayoyin da muka yi muku.

Kwarin Jiuzhaigou yana shiyya mai cin gashin kanta ta kabilun Zang da Qiang ta Aba da ke yammacin lardin Sichuan na kasar Sin, siffarsa ta yi kama da harafin Turanci na 'Y'. An nada wannan kwari mai zurfin kilomita fiye da 40 da sunan kwarin Jiuzhaigou saboda ana kasancewa da kauyuka 9 na kabilar Zang a wurin.


1  2  3  4