Darasi na 24 A Kantin Sayar da Litattafai

 Hira da CRI
 

A lokacin da kake buga waya da abokanka na }asar Sin, kullum suna cewa, sai ka zo gidana don yin ziyara a lokacin hutu, da kuma sauran maganganu kamar haka. Sun ce haka ne don nuna maka abokantaka, amma wannan bai nuna cewa, sun gayyace ka a rubuce ba. A }asar Sin, an kai ziyara ga gidaje na abokai ko dangogi sakai-sakai, kullum ba ka bukatar tabbatar da lokacin kai ziyara ga ba}inka. Idan kana son kai ziyara ga saura, sai ka gaya musu a gaba, kuma kana zuwa gidajensu in suna da lokaci. Bisa }ara saurin taki na zaman rayuwa ta zamani, da kuma bun}asuwar da ake samu wajen hanyoyin sa]arwa, ayyukan kai ziyara a tsakanin abokai da dangogi suna ta }aru, a maimakon haka kuma, a kan yin cu]anya ta hanyoyin aika da sa}o na oba-oba, da kuma E-mail, da dai sauransu. A lokacin bikin bazara na shekarar 2008, sakwannin da jama’ar dukkan }asar Sin suka aika da su, don taya murnar bikin sun kai biliyan 15.