Jin Xiaoli daya ce daga cikin manajojin kamfanin yayata al’adu da harkokin yawon bude ido na Yayun a kauyen Yunlong na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. A matsayinta na ‘yar asalin Yunlong, Jin ta yi farin cikin ganin cewa, al’adar kauyensu na noman bishiyoyin Mulberry da kiwon tsutsotsi masu samar da siliki wani muhimmin aiki ne dake wakiltar kiwon tsutsotsin da fasahar saka siliki ta kasar Sin, wanda a shekarar 2009, aka sanya cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyakin ba da dan adam ya gada, na hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD ta UNESCO.
10-Feb-2025
07-Feb-2025
A cikin wani yankin duwatsu dake lardin Guizhou, an shirya wata gasa ta kwallon kafa wadda ake yiwa lakabi da "Cun Chao", tsakanin al’ummun yankin ba tare da la’akari da kwarewa ba. Gasar Cun Chao ta sa kaimi ga wasan kwallon kafa ta yadda zai sake samun karbuwa a kasar Sin, kana ya wanzar da shahararsa a dogon lokaci ba kamar sauran wasanni ba. A halin yanzu, ana ci gaba da kokarin neman kyautata tsarin raya Cun Chao, don kiyaye gudanar da gasar cikin nasara mai dorewa.
06-Feb-2025
05-Feb-2025