2020-11-11 20:01:51 cri |
Wang Wenbin ya jadadda cewa, muddin kasashe suka martaba manufar bude kofa da yin hadin gwiwa yadda ya kamata, hakika za a iya magance tasirin annobar COVID-19 nan da nan, har ma a kai ga dawo da tattalin arzikin duniya bisa turba bayan annobar.
A yau ne kuma zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a, ya tattauna tare da amincewa kan dokar soke mambobin majalisar dokokin yankin musamman na Hong Kong wadanda suke yunkurin rarraba kasar Sin. Da yake karin haske yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, Wang Wenbin, ya bayyana cewa, an yanke shawarar ce, domin martaba da ma inganta tsarin nan na "kasa daya, tsarin mulkin iri biyu", da aiwatar da muhimmiyar dokar yankin Hong Kong da ka'idojin dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, da sauran ka'idojin doka da su ma suka wajaba a kiyaye a yankin na Hong Kong da sauran dokoki dake kunshe cikin kundin dokokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China