Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi maraba da sake bude zirga zirgar jiragen sama a kudancin Libya
2020-11-09 13:30:27        cri
Tawagar MDD mai wanzar da zaman lafiya a kasar Libya ko UNSMIL a takaice, ta yi maraba da sake bude zirga zirgar jiragen sama a kudancin kasar.

UNSMIL ta ce kudurin maido da zirga zirgar jiragen sama a kudancin Libya abu ne da ya dace, ko da yake a hannu guda kuma, tawagar ta yi tir da yadda a baya bayan nan, wasu masu dauke da makamai suka yi awon gaba da wasu fasinjoji a filin jiragen saman Mitiga na birnin Tripoli, bayan tasowar mutanen daga filin jirgin sama dake gabashin kasar.

UNSMIL ta bayyana kame mutanen a matsayin mataki da ya sabawa dokokin kasa da kasa. Da yake tsokaci game da hakan a ranar Juma'a, ministan cikin gidan kasar bangaren gwamnatin da MDD ke marawa baya, ya yi Allah wadai da kamen, yana mai cewa wadanda suka yi awon gaba da fasinjojin ba su da alaka da ma'aikatar tsaron kasar, don haka ya bukaci a yi bincike kan aukuwar lamarin.

A cewar kwamitin kare hakkin bil Adama dake kasar, an kame mutanen ne saboda yankin da suka fito, da nasabar su, da batun siyasa da matsayin su cikin al'umma.

Cikin wata sanarwa da UNSMIL ta fitar, ta ce matakin bude zirga zirgar jiragen sama a yankin na Libya, sakamako ne na nasarar da aka samu yayin zaman tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka amincewa, a ranar 23 ga watan Oktoba, da kuma zaman hadin gwiwar majalissar sojojin kasar a birnin Ghadames, na kudu maso yammacin kasar, a ranekun 2 zuwa 4 ga watan Nuwambar nan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China