Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin gina layin dogon Sichuan-Tibet mai inganci
2020-11-08 16:44:50        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin gina wani sabon layin dogo mai inganci sosai, wanda zai hade lardin Sichuan da jihar Tibet dake yammacin kasar.

Shugaban ya yi wannan furuci ne, kafin a kaddamar da aikin gina wani bangaren layin dogon, da ya hada Ya'an na lardin Sichuan, da Nyingchi na jihar Tibet a yau Lahadi.

A cewar shugaban, sabon layin dogon zai taimakawa kokarin raya yankunan yammacin kasar, musamman ma lardin Sichuan, da jihar Tibet. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China