Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aikewa John Magufuli sakon taya murnar lashe zabe
2020-11-05 19:54:34        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa John Pombe Magufuli, sakon taya murnar sake lashe zaben shugabancin Tanzania. Cikin sakon da ya aike ga shugaba Magufuli a Alhamis din nan, Xi ya ce Sin da Tanzania abokai ne na gari, masu hadin gwiwa tare, kuma 'yan uwan juna, suna kuma karfafa kawancen su sannu a hankali, tare da gudanar da musaya da hadin gwiwa a sassa masu yawa, tare da samun sabbin nasarori.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, sassan biyu suna goyon bayan juna a yakin da suke yi da cutar COVID-19. Ya ce "Ina dora muhimmancin gaske ga muhimmancin da ke akwai, don gane da ci gaban kawancen Sin da Tanzania, kuma a shirye nake na yi aiki tare da shugaba Magufuli, don kara ingiza ci gaban cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa da aiki tare tsakanin mu, ta yadda za mu samarwa al'ummun karin moriya". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China