Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kada Amurka ta lalata hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci
2020-11-06 20:39:06        cri

Game da kudurin fitar da kungiyar 'yan ta'adda ta gabashin Turkiyya ETIM daga sunayen kungiyoyin ta'addanci da Amurka ta ayyana yi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana yau a nan birnin Beijing cewa, ya kamata Amurka ta gyara kuskurenta nan take, don kada ta lalata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin yaki da ta'addanci.

Rahotanni sun nuna cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wani labari a shafin yanar gizonta a jiya, inda sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya sanar da cewa, Amurka za ta soke sunan kungiyar 'yan ta'adda ta gabashin Turkiyya ETIM, daga sunayen kungiyoyin ta'addanci, kan wannan, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna rashin jin dadi matuka da adawa ga kudurin.

Wang ya kara da cewa, yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta gabashin Turkiyya ETIM, kuduri ne da kasashen duniya suka cimma, kuma Amurka ita ma ta taba gabatar da shawarar shigar da kungiyar, cikin sunayen kungiyoyin ta'addanci yayin taron kwamitin sulhun MDD, amma yanzu ta tsai da wani kudurin da bai dace ba, lamarin da ya nuna cewa, tana amfani da ma'auni guda biyu kan batun yaki da ta'addanci. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China