Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman FDI na Sin sun doshi dala biliyan 690 tsakanin 2016 zuwa 2020
2020-11-05 21:15:16        cri

Alkaluman kididdigar kudaden da ake shigarwa Sin na jarin waje ko FDI na iya kaiwa dalar Amurka biliyan 690 tsakanin shekarun 2016 zuwa 2020 din nan, kamar dai yadda bayanin kididdiga na ma'aikatar cinikayyar kasar ya nuna.

Bayanin na alkaluman FDI ya kara da cewa, cikin rubu'i 3 na farkon shekarar nan, kudaden jarin waje da aka zubawa Sin sun karu a shekara guda da kaso 2.5 bisa dari, inda yawan su ya kai dala biliyan 103.26.

Ma'aikatar cinikayyar Sin ta fitar da bayanin ne, yayin bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin karo na uku wato CIIE, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Shanghai.

A cewar jami'in ma'aikatar cinikayyar Sin Zong Changqing, karbuwar da Sin ke da ita a fannin jawo manyan fannonin jarin waje ba ta sauya ba, ana kuma hasashe, da karfin gwiwar ganin karin masu jarin waje sun ci gaba da zubawa kasar jari cikin dogon lokaci, yayin da hada hada a fannin ke ci gaba da gudana ba tare da tsaiko ba.

Yayin da ake fuskantar raguwa a fannin shigar da kudade a wannan fanni, musamman a 'yan shekarun baya bayan nan, kason FDI na Sin tsakanin takwarorin sa na sauran sassan duniya, ya karu daga kaso 6.6% a shekarar 2015 zuwa kaso 9.2% a shekarar 2019, kana ana fatan adadin zai karu a wannan shekara ta bana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China