Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta riga ta daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashe 138 bisa shawarar ziri daya da hanya daya
2020-11-05 20:15:43        cri

A yau Alhamis kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai cewa, kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashe 138 bisa shawarar ziri daya da hanya daya, inda suke gudanar da ayyuka sama da 2000, tare kuma da samar da guraben ayyukan yi ga dubban mutane.

Wang Wenbin ya kara da cewa, a ranar 3 ga wata, an fitar da "rahoton bincike kan kimar kamfanonin kasar Sin dake gudanar da harkokinsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya a ketare, na shekarar 2020", yayin dandalin tattaunawar koli kan kimar kamfanonin kasar Sin dake ketare na shekarar 2020, inda aka bayyana sakamakon binciken da suka samu, bayan da suka yi bincike a kasashe 12 dake nahiyoyin Asiya, da Afirka da Turai, wadanda suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya.

Sakamakon ya nuna cewa, kaso 78 bisa dari na mutanen da aka ji ta bakin su, sun yaba da ayyukan kamfanonin kasar Sin, musamman ma kokarin da suke a bangaren yaki da annobar cutar COVID-19, kuma sama da kaso 50 bisa dari suna ganin cewa, kokarin da kamfanonin kasar Sin suke yi, ya kyautata manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a kasashensu, haka kuma ya samar da goyon baya gare su, a bangarorin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da samar da kayayyakin kiwon lafiya da sauransu. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China