Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Al'ummar Cote d 'Ivoire za ta iya wanzar da daidaito da ciyar da kasar gaba
2020-11-05 20:12:17        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na bibiyar yanayin da ake ciki, bayan babban zaben shugabancin kasar Cote d 'Ivoire, ta kuma yi imanin cewa, al'ummar Cote d 'Ivoire na da iko, da wayewar da ake bukata, don daidaita al'amuran kasa da wanzar da ci gaba. Wang Wenbin ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa.

A ranar Talata ne dai, hukumar zaben kasar Cote d 'Ivoire mai zaman kan ta, ta ayyana shugaban kasar mai ci wato Alassane Ouattara, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da kaso 94.27 bisa dari, na daukacin kuri'un da aka kada.

To sai dai kuma an fuskanci wasu tashe tashen hankula yayin da babban zaben ke gudana, wanda hakan ya jawo hankalin sassan kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China