Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: A bana abokan huldar shawarar ziri daya da hanya daya sun tsara shirye shiryen hadin gwiwa a sassa da dama
2020-11-04 20:09:19        cri

Kakakin ma'aikatar wajen Sin Wang Wenbin, ya ce duk da tasirin cutar COVID-19 a fannin musaya tsakanin kasa da kasa, abokan hulda karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, sun kafa tsare tsaren hadin gwiwa a sassa masu yawa, sun kuma gudanar da tarukan karawa juna sani na kasa da kasa, a zahiri da kuma ta yanar gizo sama da 20.

Wang wanda ya bayyana hakan yau Laraba, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce shawarar ziri daya da hanya daya, ta biyo bayan zuzzurfar tattaunawa, da gudummawar hadin gwiwa, da burin samun riba tare, tare da goyon bayan cudanyar sassa daban daban.

Ya ce, "Mun amince cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, wadda ta shafi sassan kasa da kasa, za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen gina ziri daya da hanya daya mai nagarta, wanda zai tallafawa dukkanin abokan hulda wajen yaki da cutar COVID-19, ta habaka tattalin arziki, da farfado da yanayin zamantakewar al'umma, tare da aiwatar da ajandar MDD ta wanzar da ci gaban duniya nan da shekarar 2030." (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China