Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwadibwa ta tura wata babbar tawaga don halartar bikin baje-kolin tattalin arziki da kasuwanci na Sin da Afirka
2019-06-27 11:05:47        cri

Hadin-gwiwar Sin da Kwadibwa dake yammacin Afirka na bunkasa cikin sauri a 'yan shekarun nan. A matsayinta na daya daga cikin kasashe shida wadanda za su yi gagarumin bikin nuna al'adunsu na musamman a wajen taron baje-kolin tattalin arziki da kasuwanci karo na farko tsakanin Sin da Afirka wanda aka bude yau Alhamis a birnin Changsha na kasar Sin, Kwadibwa ta tura wata babbar tawaga dake kunshe da ministoci guda uku don halartar bikin. Ministan kula da sana'o'in hannu na Kwadibwa, wanda daya ne daga cikin shugabannin tawagar, Sidiki Konate ya ce, alakar Sin da kasarsa ta fannin tattalin arziki da kasuwanci na da kyau sosai, yana kuma fatan bikin baje-kolin zai baiwa Kwadibwa damar tallata kanta, da yin koyi da kasar Sin a fannin neman bunkasuwa.

Sidiki Konate ya ce, ba babbar kasar noma a yammacin Afirka kadai Kwadibwa ke da ita ba, har ma da dimbin albarkatun ma'adinai da aka hore mata, kana, yawan GDPn kasar ya kai kaso 40 bisa dari na kawancen tattalin arziki da takardun kudade na kasashen yammacin Afirka ko kuma UMOA a takaice. Don haka, kamata ya yi Kwadibwa ta yi amfani da wannan kyakkyawar dama don fadada hadin-gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China