Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin CIIE ya shaida karfin Sin na ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba
2020-11-05 16:28:07        cri

Ga duk mai bibiyar kafofin watsa labarai, ba zai rasa ganin yadda aka bude bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na uku a birnin Shanghai ba.

Idan mun lura da jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin bikin bude baje kolin, za mu iya lura da yadda ya bayyana sabbin matakai da kasarsa za ta aiwatar a fannin bude kofa ga kasashen waje daga dukkanin fannoni, a wani mataki na "A gudu tare a tsira tare".

Baya ga batun bude kofa, akwai sauran muhimman kudurorin raya kasa da mahukuntan na Sin suka ayyana aiwatarwa, ciki hadda ci gaba da kyautata yanayin zuba jarin waje a cikin kasar, da fannin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa, da raya tattalin arziki ta amfani da fasahohin zamani na yanar gizo, da zurfafa sauye-sauye, da kirkire-kirkire a fannin cinikayya da zuba jari, da sakarwa kasuwa mara, da sai sauran su.

Idan mun lura da kyau, wannan baje koli na CIIE, zai ba da wata dama ta tabbatarwa dukkanin duniya cewa, manufofin ci gaban tattalin arziki na kasar Sin ba za su sauya ba, kuma tarin kalubale da kasar, da ma sauran sassan duniya ke fuskanta masu nasaba da yaki da cutar COVID-19, ba za su zamewa kasar Sin birki, na dakatar da ci gaban ta ba.

Hasali ma, mun ga yadda bikin na bana, ya samu karin mahalarta daga kamfanoni, masana'antu, 'yan kasuwa da wakilan gwamnatoci, ciki hadda na nahiyar Afirka, wadanda suka jinjinawa kwazon Sin na rungumar kasashen duniya, a kokarin da ake yi na cimma nasara tare.

A jumlace, muna iya cewa, shawo kan cutar COVID-19 da kasar Sin ta yi, da kokarinta na tabbatar da ci gaban tattalin arziki a cikin gida, da yunkurinta na kara bude kofa ga waje, da gudanar da wannan baje koli na CIIE a wannan gaba da duniya ke fuskantar manyan kalubale, alamu ne dake tabbatar da cewa, tana da karfin ikon ci gaba da aiwatar da manufofinta na ci gaba kamar yadda aka tsara. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China