Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bayyana damuwa game da rikicin da ake a Habasha
2020-11-05 10:00:34        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa game da rikici da ake a yankin Tigray na Habasha, inda ya yi kira da a gaggauta daukar matakan shawo kan lamarin tare da tabbatar da sulhunta rikicin cikin lumana.

A jiya Laraba, Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya bada umarnin daukar matakan soji kan kungiyar 'yan tawaye mai rajin 'yantar da al'ummar Tigray wato TPLF dake jihar Tigray na arewacin kasar, a wani mataki na mayar da martani ga harin da aka kai wa wani sansanin soji a jiyan. Har ila yau a jiyan, majalisar ministocin kasar ta ayyana dokar ta baci na tsawon watanni 6 a yankin na Tigray dake arewacin kasar.

A makonnin baya-bayan nan, ana ta samun karuwar tankiya tsakanin jam'iyyar Prosperity ta Firaminista Ahmed da kuma kungiyar TPLF, inda dukkaninsu ke zargin juna da kokarin hargitsa kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China