Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin ranar birane ta duniya ta shekarar 2020 a duk fadin kasar Sin
2020-11-01 16:51:44        cri

Biranen kasar Sin da suka hada da Fuzhou da Shanghai sun gudanar da bukukuwan murnar zagayowar ranar birane ta kasa da kasa karo na bakwai.

Taken bikin na bana shi ne, "Martaba unguwanni da biranen mu", bikin na wannan shekarar ya samu halartar jami'an gwamnati, da kwararru da wakilan al'ummomi daga cikin gida da ketare, domin musayar kwarewar da suka samu wajen daga matsayin samar da ingantaccen ci gaban birane da inganta rayuwar al'umma.

Jiang Wanrong, mataimakin ministan samar da gidaje da raya ci gaban birane na kasar Sin, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, tun bayan kafuwarta, ranar birane ta kasa da kasa tana kara samun karbuwa a duniya da kuma taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ajandar samar da dawwamammen ci gaban duniya nan da shekarar 2030 da sabuwar ajandar raya birane.

Jiang, ya bayyana a lokacin bikin wanda aka gudanar a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwarta da sauran kasashen duniya a fannin ayyukan gina gidaje da raya birane da yankunan karkara, da yin musayar kwarewa ta zahiri da amfani da fasahohin kirkire kirkire domin gina ingantattun birane da unguwanni.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China