Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jiragen sama a kasar Sin yana farfadowa sosai
2020-10-28 21:55:36        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar sufuri ta kasar Sin Wu Chungeng ya bayyana a yau Laraba cewa, zuwa watan Satumbar bana, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jiragen sama a cikin kasar ya farfado sosai, inda ya kai kaso 98.

Mista Wu ya ce, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta hanyoyin jiragen kasa da na sama yana farfadowa cikin sauri, al'amarin da ya shaida cewa, tattalin arzikin kasar na tafiya yadda ya kamata, kana, ya karfafa imanin sana'ar zirga-zirga ta kasar, wato za ta iya kammala burin da aka tsara a bana da tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikinta yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China