Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya ba da jawabi a dandalin fitattun masu nazarin kimiyya da fasaha
2020-10-30 10:45:39        cri

 

 

A yau Juma'a ne aka kaddamar da dandalin fitattun masu nazarin kimiyya da fasaha na duniya karo na 3 a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi ta kafar bidiyo.

A cewar shugaban, tun bayan barkewar annobar COVID-19 a duniya, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, sun yi hadin gwiwa sosai don neman dabarar dakile cutar, inda suka gudanar da nazari na musamman, da hadin kai a tsakanin kasashe daban daban, a fannonin jinyar masu dauke da cutar, da samar da magani, da allurar rigakafi, da hana bazuwar cutar, da dai sauransu, tare da samar da babbar gudunmawa ga aikin dakile annobar.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, kasar Sin tana dora matukar muhimmanci kan aikin raya fasahohin zamani, da kirkiro sabbin fasahohi, kana tana kokarin yin amfani da sabbin fasahohin da aka kirkiro wajen ciyar da tattalin arziki gaba. A fannin hadin gwiwa ta fuskar kimiyya da fasaha kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga sauran kasashe, gami da neman tabbatar da moriyar bangarori daban daban.

Shugaba Xi ya yi fatan ganin kwararrun masu nazarin kimiyya da fasaha mahalarta taron, za su sanya himma wajen musayar ra'ayoyinsu, da hadin kai a tsakaninsu, don taimakawa raya harkar kimiyya da fasaha ta duniya.

Dandalin da ake gudanarwa a wannan karo yana da jigon "Raya kimiyya da fasaha don tabbatar da makoma mai haske ta daukacin bil Adama", ya kuma samu halartar masu nazarin kimiyya da fasaha fiye da 300, daga kasashe daban daban, ciki har da wasu 61 da suka taba samun kyautar yabo ta Nobel. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China