![]() |
|
2020-10-30 10:02:50 cri |
Wasu masanan Afirka suna ganin cewa, shawarwarin da aka gabatar game da tsara shirin, suna cike da hangen nesa, da sanin burin da ake son cimmawa, wanda ya bude sabon babi na raya kasa ta zamani mai tsarin gurguzu, da kara imanin kasa da kasa kan bunkasuwar kasar Sin, da kuma taimakawa farfado da tattalin arzikin duniya yayin da ake tinkarar cutar COVID-19.
Masanin kula da batun kasa da kasa na kasar Kenya Cavins Adhill ya bayyana cewa, a lokacin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar karo na 13, Sin ta samu manyan nasarori a fannin yaki da talauci, da kiyaye muhalli, da tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da sauransu, wanda hakan ya samar da muhimmiyar gudummawa kan samun bunkasuwa mai dorewa a duniya.
A yayin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar karo na 14, an yi imani da cewa, Sin za ta kafa sabon tsarin tattalin arziki mai bude kofa, da samun sabon ci gaba kan kiyaye muhalli, wadanda za su zama abun misali ga sauran kasashen duniya, kana za a sa kaimi ga samun bunkasuwa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance a duniya ba.
Farfesan tattalin arziki da hada-hadar kudi na jami'ar Cairo ta kasar Masar Waleed Gaballah, ya bayyana cewa, shawarwarin tsara shirin sun jaddada kafa hanyoyin samar da kayayyaki ba tare da gurbata yanayi ba, da gabatar da burin samun bunkasuwa tare da kiyaye muhalli. Ya ce Sin za ta kara tabbatar da yaki da talauci, da kuma samar da gudummawa wajen cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa na MDD.
Shugaban kungiyar kula da hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin, da samun bunkasuwa ta kasar Morocco Nasser Bouchiba ya bayyana cewa, ya kamata kasashe masu tasowa, su koyi fasahohin tsarin samun bunkasuwa na kasar Sin. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China