Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika na iya daukar darasi daga kokarin Sin na kare albarkatun daji
2020-10-10 17:37:13        cri
Gidauniyar kula da namun daji ta Afrika, ta ce nahiyar na iya daukar darasi daga kokarin kasar Sin a fannin kula da albarkatun daji.

Mataimakin shugaban gidauniyar Fred Kumah, ya shaidawa Xinhua a Nairobi cewa, kasar Sin ta yi amfani da matakan da suka kunshi kare dabbobin daji da kuma amfani da al'umma wajen cimma nasara a fannin, wanda ke bukatar nahiyar Afrika ta mayar da hankali kai.

A cewarsa, mayar da hankali kan kula da muhallin halittu da kare muhallin daga lalacewa shi ne mataki na gaba kuma mai muhimmanci wajen kare albarkatun daji a nahiyar.

Fred Kumah ya kara da cewa, galibin kasashen nahiyar na bukatar tsarukan farfado da nau'ikan dake fuskantar bazaranar bacewa, saboda zai taimaka wajen jan hankalin masu ruwa da tsaki su tallafawa dabarun da za su kai ga samun sakamakon da ake muradi.

Ya kara da cewa, annobar COVID-19 ta haifar da kalubale a kan dukkan bangarorin rayuwa, musammam bangaren kare albarkatun daji, inda dabarun killacewa suka yi tasiri kan kudaden shigar da ake samu daga yawon bude ido. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China