Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko 'Yan Siyasan Amurka Na Son Hura Wuta A Yankin Taiwan Na Sin? Hakan ba zai yi nasara Ba!
2020-10-29 15:42:10        cri

Bayan kasar Amurka ta zartas da shirin sayar da makamai iri uku ga yankin Taiwan na kasar Sin a makon da ya gabata, gwamnatin kasar Amurka ta zartas da kudurin sayar da makaman kare gabar teku ga yankin na Taiwan a kwanan baya.

Ga alama burin kasar Amurka shi ne, kawo sabani a tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan, ta hanyar sayar da makamai ga sojojin yankin na Taiwan a wannan shekarar da za ta gudanar da babban zaben shugaban kasarta. Kasar Amurka tana son kawar da hankulan al'ummomin kasarta ta hanyar nuna karfinta kan kasar Sin, sa'an nan, ta nuna burin ta a fili na hana bunkasuwar kasar Sin. Amma ko shakka babu, ba za ta cimma nasarar wannan buri ba!

Sanin kowa ne, kiyaye ka'idar "kasar Sin daya tak a duniya" shi ne babban tushen raya dangantakar siyasa dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Kaza lika batun Taiwan batu ne dake shafar muhimmiyar moriyar kasar Sin, amma, wasu 'yan siyasan gwamnatin kasar Amurka na wannan karo, su kan nuna goyo baya ga masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin, lamarin da ya haddasa karin sabani tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.

Musamman ma a kwanan baya, kasar Amurkan ta yi ta tsoma baki cikin harkokin Taiwan, ta kuma tura manyan jami'anta zuwa yankin domin gudanar da ziyarar aiki, zuwa sayar da makamai ga yankin. A hakika dai, kasar Amurka tana son matsa wa kasar Sin lamba ta wadannan hanyoyi.

Al'ummomin kasar Sin al'ummomi masu son zaman lafiya, amma, ba za su yi hakuri kan wadanda suke neman bata 'yancin kai, da tsaron kasarsu ba. Kwanan baya, Kasar Sin ta fara mai da martani ga kasar Amurka, inda ta sanar da cewa, za ta kakaba wa kamfanonin Amurka da suka sayar da makamai ga yankin Taiwan, ko masu nasaba da batun takunkumi.

Kasar Sin tana gargadi ga kasar Amurka, da ta duba halin da take ciki, ta soke shirin sayar da makamai ga sojojin yankin Taiwan, sa'an nan, ta tsayar da dukkanin mu'amalar harkokin soja dake tsakaninta da yankin Taiwan na kasar Sin, musamman ma, neman hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar raya dangantakar dake tsakaninta da yankin Taiwan na kasar ta Sin.

Al'ummomin kasar Sin ba za su yi hakuri kan wadanda suke neman bata 'yancin kai, da tsaro da bunkasuwar kasar su ba. Tabbas ne, wadanda suke neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin za su girbe mummunan sakamakon aiki da suka yi. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China