Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Maaikata yan ci rani na Xinjiang na aiki ne domin samun rayuwa mai inganci
2020-10-28 10:54:23        cri

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa, ma'aikata 'yan ci rani na jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, na gudanar da ayyukan kwadago ne domin samun damar kyautata rayuwar su, da kara fadada damar su ta ci gaba, suna kuma aiki ne bisa radin kan su.

Rahoton dai na kunshe ne da cikakkun bayanai da aka tattara daga wurare daban daban, da takardun tambayoyi da mutane suka amsa, da ganawa da mutane kai tsaye, kuma wata tawagar masu bincike a cibiyar kare hakkin bil Adama dake jami'ar kimiyyar siyasa da shari'a ta "Southwest" dake Sin ce ta gudanar da shi.

Masu binciken dai sun yiwa rahoton lakabi da "Bincike game da halin da ake ciki a Xinjiang game da daukacin kabilu daban daban 'yan ci ranin yankin masu ayyukan kwadago". Rahoton ya ce, wadannan rukunoni na 'yan kwadago na jihar Xinjiang, na aiki ne bisa zabin kan su, gwargwadon halin da suke ciki, wanda hakan ke share musu fagen samun ci gaba a rayuwar su.

A daya hannun kuma, kudaden shigar wata wata na 'yan kwadagon, da jimillar kudaden da iyalan su ke samu a duk shekara na karuwa matuka, bayan gudanar da ayyukan kwadago.

Bugu da kari, rahoton ya ce akwai dokoki da ka'idoji dake kare hakkoki da moriyar 'yan kwadagon, wanda hakan ke samar da cikakkiyar kariya daga sanya su yin aikin dole.

Daga nan sai rahoton ya yi watsi da zarge zargen da wasu sassan yammacin duniya ke yi, cewa wai ana sanya 'yan kwadago daga jihar ta Xinjiang yin aikin dole, wanda hakan ya jirkita manufar kasar Sin ta yaki da fatara, da bunkasa samar da guraben ayyuka. Rahoton ya ce wadannan sassa ba su yi la'akari da bukatun al'ummar Xinjiang ba, ta neman rayuwa mai cike da farin ciki da walwala. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China