Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton bincike kan aikin kananan kabilu a yankin Xinjiang
2020-10-20 15:27:36        cri

A kwanakin baya ne, wasu masana daga kasashen yamma suka wallafa wasu rahotanni dake cewa, wai ana samun karuwar tilasta aikin kwadago a yankin Xinjiang na kasar Sin, kana wasu 'yan siyasar yammacin duniya ma, na ikirarin cewa, "Ana tilasta aikin kwagado a Xinjiang". Don haka, akwai zargin tilasta aikin kwadago a Xinjiang? Kan wannan batu, cibiyar bincike dake Xinjiang, ta gayyaci kwararru da masana, domin su bincike yadda kananan kabilu ke gudanar da aikin kwadago a yankin na Xinjiang.

Tawagar bincike dai, ta ziyarci sama da kamfanoni 70, da kamfanonin gama kai dake yankunan karkara da wuraren sana'o'i na daidaikun mutane da aka kafa a Ili, da Karamaya, da Shihezi, da Kashgar da Hotan, da Kizilsu da kuma Aksu dake Xinjiang da kuma birane dake wajen shiyyar, kamar Beijing da Tianjin.

Sun kuma tattauna tare da hira da sama da manajojin kamfanoni da ma'aikata da masu sana'o'i masu zaman kansu da ma'aikata kananan kabilu sama da 800, sun kuma nazarci muhimman takardun gwamnati 26 da aka gabatar tun a shekarar 2016, da takardun da abin ya shafa 48 da masana suka wallafa tun a shekarar 2005.

Daga karshe, tawagar ta bayyana cewa, gwamnatoci a dukkan matakai da kamfanonin da abin ya shafa a Xinjiang da sauran larduna ko birane, sun taimakawa 'yan kananan kabilu samun guraben ayyukan yi, sun kuma kare dukkan hakkokinsu, kamar 'yancin samun aikin yi da na ci gaba. Rukunin kananan kabilu suna aiki ne bisa radin kansu, sun kuma zabi kafa sana'o'insu na kansu, don haka batun wai, ana tilastawa mutane aikin kwadago, bai ma taso ba. Zargin da wasu masanan kasashen yamma ke yi, karye ce kawai, kuma ikirarin da suke yi kan wannan batu, ba shi da tushe balle makama. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China