Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta Sin ta samu karuwar yan kabilar Uygur
2020-09-04 15:27:49        cri

Yawan 'yan kabilar Uygur na jihar Xinjiang mai cin gashin kai, dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin ya karu da miliyan 2.55, inda a jimlace ya kai miliyan 12.72 cikin shekaru takwas wato daga shekarar 2010 zuwa 2018, an samu karinsu da kashi 25.04 bisa 100, hukumomin yankin ne suka tabbatar da lamarin.

Wasu alkaluman kididdiga da gwamnatin jihar ta fitar sun nuna cewa, adadin 'yan kabilar Uygur yana karuwa fiye da na sauran kabilun dake yankin. A cikin wannan wa'adi kuma, adadin 'yan kabilar Han shi ma a wannan yanki ya karu da kashi 2 bisa 100 zuwa kimanin miliyan 9.

Adadin 'yan kabilar Uygur a jihar Xinjiang bai wuce miliyan 3 ba a shekarar 1953, a lokacin da kasar Sin ta gudanar da kidayar jama'arta a karon farko a duk fadin kasar. A yanzu, yawan 'yan kabilar Uygur ya ninka har sau hudu idan an kwatanta da yawansu a wancan lokacin.

Adadin haihuwar 'yan kabilar daga shekarar 2010 zuwa 2018 yana karuwa ne da kashi 11.9 a cikin mutane 1,000, ya zarce na 'yan kabilar Han wanda ke karuwa da kashi 9.42 cikin mutane 1,000, kamar yadda jami'ar hukumar kididdiga ta jihar Xinjiang, Tursunnay Abudurayim, ta bayyana.

Ta ce, ana tabbatar da 'yancin haihuwa da kula da lafiyar 'yan kananan kabilu, ciki har da na 'yan kabilar Uygur a jihar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China