Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Hadin gwiwa ne kadai hanyar shawo kan cutar COVID-19 da kalubalen sauyin yanayi
2020-10-27 11:27:06        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce hadin gwiwar sassan kasa da kasa ne kadai hanyar da za a iya bi, wajen shawo kan kalubalen cutar numfashi ta COVID-19, da ma mummunan tasirin sauyin yanayi.

Mr. Guterres wanda ya gabatar da jawabi a jiya Litinin, yayin taron gama gari na majalissar albarkacin ranar tunawa da kafuwar MDDr, ya ce matakin zai taimaka wajen rage fadadar gibi tsakanin al'ummu, da bazuwar halayyar nuna kin jinin juna.

Ya ce "A wannan gaba da ake fuskantar babban kalubale, ina maraba da kudurin wannan zaure, na sake ingiza goyon baya ga cudanyar sassa daban daban, ina kuma fatan ganin shigar kowa da kowa, da aiki tare, don karfafa jagorancin duniya, da kuma kwazon duniya baki daya, wajen tunkarar kalubale na yanzu da ma wadanda za su zo nan gaba.

MDD ta kebe ranar 24 ga watan Oktobar ko wace shekara, domin bikin tunawa da kafuwar ta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China