Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Libya
2020-10-24 16:59:06        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin Libya suka yi a Geneva, karkashin jagorancin majalisar.

Antonio Guterres, ya shaidawa manema labarai a hedkwatar majalisar dake birnin New York cewa, wannan mataki ne mai matukar muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Libya. Kuma yana taya bangarorin murna, wadanda, suka sanya muradun kasarsu gaba da sabanin dake tsakaninsu.

Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a kasar da ma yankin, da su mutunta tanade-tanaden yarjejeniyar da tabbatar da aiwatar da ita, ba tare da bata lokaci ba.

Har ila yau, ya yi kira ga kasa da kasa su marawa al'ummar Libya baya wajen tsagaita bude wutar tare da kawo karshen rikicin. Yana mai cewa, wannan ya kunshi mutunta takunkumin makamai da kwamitin sulhu na majalisar ya kakabawa Libya ba tare da wani sharadi ko uzuri ba.

Sakatare Janar din ya kuma bukaci bangarorin sun rike wannan karfi da jajircewa da suka nuna, wajen cimma maslaha a siyasance, da warware batutuwan da suka shafi tattalin arziki da shawo kan yanayin jin kai a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China