Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya saurari ra'ayoyin bangarori daban daban don tsara wata manufar raya kasa
2020-10-27 10:57:06        cri

 

 

 

Yanzu haka ana gudanar da cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na 19 a kasar, inda manyan shugabannin kasar ke tattaunawa kan shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 14. Sai dai kafin wannan taro, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira tarukan karawa juna sani, da ziyartar wurare daban daban, don sauraron ra'ayoyin mutane masu sana'o'i daban daban dangane da shirin raya kasa, ta yadda yake neman tabbatar da muhimmancin ra'ayoyin al'ummun kasar a cikin manufar ta raya kasa.

 

 

Tarukan karawa juna sani da shugaban ya kira sun hada da, taron masu kamfanoni da aka shirya a ranar 21 ga watan Yulin bana, da taron masana ilimin tattalin arziki da zaman al'umma da aka shirya a ranar 24 ga watan Agustan bana, da taron masu nazarin kimiyya da fasaha da aka shirya a ranar 11 ga watan Satumban bana, da taron kwararru masu sana'o'in aikin malanta, da al'adu, da kiwon lafiya, da kuma wasannin motsa jiki da aka shirya a ranar 22 ga watan Satumban bana, da dai makamantansu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China