Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya amsa wasikar da malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin suka aike masa
2020-10-25 16:34:23        cri

A ranar 23 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping ya amshi wasikar da malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin suka aike masa, inda ya yaba da kokarin da suke don raya fasahar wasannin gargajiyar kasar ta Sin.

Xi ya jaddada cewa, wasannin gargajiyar kasar Sin al'adun gargajiya ne masu daraja na kasar Sin, ya dace malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin su kara sanya kokari a daidai lokacin murnar cika shekaru 70 da kafa kwalejin domin ciyar da wasannin gaba yadda ya kamata.

A kwanan baya, wasu wakilan malamai da dalibai na kwalejin wasannin gargajiyar kasar Sin sun rubuta wata wasika zuwa ga babban sakatare Xi, inda suka yi bayani kan sakamakon da suka samu a cikin shekaru 70 da suka gabata, tare kuma da nuna fatansu na raya wasannin gargajiyar kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China