Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nasarar sojojin Sin ta nuna kudurin al'ummar kasar na kiyaye zaman lafiya a duniya
2020-10-23 11:36:02        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Juma'a cewa, yakin adawa da zaluncin Amurka da taimakawa Koriya ta Arewa, ya rusa shirin azzalumai na murkushe sabuwar kasar Sin.

Xi Jinping ya ce yakin turjewa zaluncin Amurka da taimakawa Koriya ta Arewa, ya nuna karfin kudurin al'ummar Sinawa na adawa da mulkin danniya.

Ya ce nasarar da sojojin sa kai na kasar Sin a yakin da aka yi tsakanin 1950 zuwa 1953, ya nuna matsayar Sinawa ta kiyaye zaman lafiya a duniya.

Ya kara da cewa, dole ne a yi kokarin koyi da ruhin wadancan sojoji 'yan sa kai daga zuri'a zuwa zuri'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China