Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin WHO: Shiga shirin COVAX ya shaida hadin gwiwar kasa da kasa
2020-10-27 10:20:57        cri
Kasar Sin ta sanar da shiga shirin COVAX da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, da kawancen shirin samar da allurar rigakafi na duniya ke jagoranta a farkon wannan wata. Game da hakan, kakakin hukumar WHO Margaret Harris, ta yi maraba da kudurin na Sin, yayin zantawar ta da wakilin kafar CMG ta kasar Sin.

Harris ta yi nuni da cewa, yaduwar cutar COVID-19 ba matsalar lafiyar jiki ce kawai ba, domin kuma matsalar ta shafi zamantakewar al'umma da tattalin arziki, wadda ta haddasa mutuwar mutane a kalla miliyan daya, kuma allurar rigakafin cutar za ta kasance muhimmin abin da zai kawo karshen cutar. Ta ce ta hanyar shirin COVAX, za a rarraba allurar rigakafi ga dukkan duniya cikin adalci, kuma ana bukatar dukkan duniya ta yi kokari tare domin cimma nasarar hakan.

Harris ta kara da cewa, Sin da sauran kasashen duniya sun shiga wannan shiri, wanda hakan ya shaida hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. Kuma game da bangarori daban daban, da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, wannan babbar nasara ce. Ko shakka babu, abu ne mai muhimmanci kasa da kasa su yi hadin gwiwa da yin kokari tare. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China