2020-10-24 16:40:39 cri |
A cewar Mista Ghebreyesus, watanni masu zuwa za su zama lokaci mai matukar wuya ta fuskar dakile cutar COVID-19, kana wasu kasashe na kan hanyar tsunduma cikin mawuyacin hali.
Ya ce, yanzu wani lokaci ne mai muhimmanci, wanda zai iya tabbatar da yanayin da ake ciki a nan gaba, musamman a wasu wuraren dake arewacin duniya.
Jami'in ya kara da cewa, yanzu ana samun karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 cikin matukar sauri a wasu kasashe da yawa, lamarin da ya sa ake fuskantar matsalar karancin gadaje da dakunan kwantar da majiyyata a asibitoci da wuraren kula da mutanen da lafiyarsu ke cikin wani yanayi mai hadari, ko da yake har yanzu ana cikin watan Oktoba.
Shugaban na WHO, ya bukaci shugabannin kasashe daban daban da su dauki kwararan matakai ba tare da wani jinkiri ba, don magance samun karuwar mace-mace, da tsaiko ga ayyukan hukumomin kula da lafiya, gami da sake kulle makarantu. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China