Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tedros: Siyasantar da cutar COVID-19 zai kara haddasa mutuwar mutane
2020-10-27 10:20:05        cri
Babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a gun taron manema labaru da hukumar ta gudanar a jiya cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 da aka gabatar bisa rahoton da kasashen duniya suka fitar a makon jiya, ya nuna yawaitar alkaluma sama da wadanda aka samu a baya, tun daga barkewar cutar.

Jami'in ya ce yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar, da masu samun jinya a asibiti a kasashe da dama na sashen arewacin duniya yana karuwa. Yanzu haka mutane dake cikin mawuyacin halin fama da cutar, na cika dakunan kula da marasa lafiya a wasu wurare, musamman a kasashen nahiyar Turai da arewacin Amurka.

Tedros ya bayyana cewa, idan shugabannin kasashen sun dauki matakai bisa shirin da aka tsara, hakan zai iya hana yaduwar cutar, amma siyasantar da cutar kuma, na iya kara haddasa mutuwar mutane. Ya ce, a wasu kasashen dake fuskantar rikicin siyasa, da rashin girmama masana kimiyya da fasaha, akwai yiwuwar kara fuskantar rikice-rikice, kana yawan mutanen da za su kamu da cutar, ko za su mutu a sakamakon cutar zai karu. Wannan dalili ne, dake wajabta dakatar da siyasantar da cutar COVID-19.

Haka zalika kuma, Tedros ya yi kira ga jama'a, da su bi matakan kandagarkin cutar masu amfani. Kana ya kamata gwamnatocin kasa da kasa su rungumi yanayin tinkarar cutar, da yanke hanyoyin yaduwar ta, da yin bincike ga dukkan mutanen da suke da alaka da cutar, da killacewa, da ba da jinya ga mutanen da suka kamu da cutar, da kuma nema da killace dukkan mutanen da suka yi cudanya da mutanen da ke dauke da ita. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China