![]() |
|
2020-10-26 20:50:48 cri |
Jiya Lahadi, rana ce da gamayyar raya kudancin Afirka wato SADC a takaice ta kebe a matsayin ranar nuna adawa da takunkumi, inda kasashen Afirka da dama suka yi kira a soke takunkumin da kasashen yamma suka sanyawa kasar Zimbabwe. Mista Zhao ya bayyana cewa, kamata ya yi Amurka da sauran kasashe da kungiyoyi, su cire takunkumin da suka sanyawa Zimbabwe, da daukar matakan da suka dace, domin taimakawa Zimbabwe yaki da annobar COVID-19, da ma farfado da tattalin arzikinta.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China