Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Gansu na Sin ya ba da gudunmawar kayan yaki da COVID-19 ga lardin yammacin Mashonaland na Zimbabwe
2020-05-07 15:39:58        cri

Lardin Gansu na kasar Sin ya kulla huldar abokantaka da lardin yammacin Mashonaland na kasar Zimbabwe ta kudancin Afrika tun a shekarar 2004. Sama da shekaru 10, hadin gwiwar abokantaka dake tsakanin lardunan biyu tana kara zurfafa, kuma ta samar da kyakkyawan sakamako a fannoni daban daban. A bisa halin da ake ciki na barkewar annobar COVID-19, lardin Gansu ya bayar da taimako ga lardin yammacin Mashonaland, tallafin sun kunshi kayan ba da kariya da za'a yi amfani da su wajen yaki da annobar COVID-19.

Kayayyakin sun hada da takunkumin rufe fuska na jami'an lafiya guda 12,000, da takunkumin samfurin KN95 guda 2,000, da samfurin N95 1,000 da kuma rigunan ba da kariya 1000. A lokacin bikin mika kayayyakin, gwamna Mary Mliswa ta lardin, ta yabawa kasar Sin bisa wannan taimako. Ta ce da ma lardin yana fama da karancin kayayyakin, kuma taimakon da suka samu daga lardin Gansu na kasar Sin ya zo lokacin da suke tsaka da bukata. Mliswa ta ce za'a rarraba kayayyakin zuwa asibitocin da aka kebe don jinyar masu fama da cutar ta COVID-19 da wasu asibitocin dake yankunan karkara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China