Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin na karfafa zuba jari a Habasha yayin da ake fama da COVID-19
2020-10-24 16:54:23        cri
Yayin da Habasha ke kokarin farfado da harkokin kasuwanci da zuba jari da suka gamu da tasirin annobar COVID-19, ayyukan kamfanonin kasar Sin sun karfafawa kasar burinta.

A cewar wasu alkaluma na baya-bayan da hukumar kula da zuba jari ta Habasha ta fitar, kasar ta samu jarin ketare na kai tsaye da ya kai dala miliyan 500 cikin watanni 3 da suka gabata, inda bangarorin samar da kayayyaki da na aikin gona da bada hidimomi suka mamaye mafi yawan kudin shigar da aka samu a rubu'in farko na shekarar kudin kasar da ya fara ranar 7 ga watan Yuli.

Kwamishinan hukumar Lelise Neme, ya shaidawa manema labarai a farkon makon nan cewa, kudin shigar da aka samu a kasar a rubu'in babu laifi, bisa la'akari da fama da ake yi da kalubalen COVID-19 wanda ke mummunan tasiri ga kasa da kasa, baya ga rikicin da ake fama da shi a wasu sassan kasar.

A cewarsa, yayin da kasar ke kokarin janyo karin jari duk da tasirin annobar a kan tattalin arziki, kamfanonin kasar Sin sun kasance wani bangare mai muhimmanci na kokarin kasar na sassauta tasirin annobar a kan bangaren zuba jari.

Kwamishinan ya kara da cewa, yanzu, kamfanonin samar da kayayyaki da dama na samar da makarin baki da hanci da safar hannu da kayayyakin gwajin cutar, lamarin da ya taimakawa shawo kan tasirin annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China