Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Habasha ya yabawa nasarorin aikin lambun shakatawar da Sin ke ginawa
2020-09-11 14:51:09        cri

Shugaban kasar Habasha Sahle-Work Zewde, ya yabawa cigaban da aka samu a aikin gina lambun shakatawa wanda kasar Sin ke gudanarwa a Addis Ababa, babban birnin kasar dake gabashin Afrika.

Da yake jawabi game da irin manyan nasarorin da aka cimma wajen gudanar da aikin gina lambun shakatawar, wanda aka yiwa lakabin Friendship Square, wani bangare ne dake karawa babban birnin kasar ta Habasha Addis Ababa kwalliya, shugaban kasar ya ce, ana gudanar da aikin ne bisa dacewa wajen kara martaba ga birnin Addis Ababa, wanda ya kasance hedkwatar siyasa na kungiyar tarayyar Afrika.

Lambun shakatawar na Friendship Square, wanda kamfanin kasar Sin CCCC ke gudanar da aikin, inda ake sa ran za a kammala cikin kasa da shekara guda. Aikin ya kunshi hecta 32 a zagayen farko.

Tan Jian, jakadan kasar Sin a Habasha ya ce, aikin na Friendship Square ya kasance tamkar wata kyauta ce ga al'ummar Habasha, wadanda ke shirin gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar kasar Habasha a ranar Juma'ar nan.

Tan ya kara da cewa, wannan gagarumin aiki, wanda kasar Sin ke ginawa kyauta a matsayin wani bangare na aikin tallafin kasar Sin, zai bunkasa tattalin arzikin kasar a fannin ayyukan hidima, kana zai kara bunkasa fannin yawon bude ido na kasar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China