Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in diflomasiyyar Habasha ya yabawa shirin hadin gwiwar yaki da  COVID-19 da kasar Sin
2020-09-05 15:23:13        cri
Wani jami'in diflomasiyyar kasar Habasha ya yabawa shirin hadin gwiwar ceto rayuka a yaki da annobar COVID-19 na kasar tare da kasar Sin.

Da yake jawabi a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Teshome Toga, jakadan Habasha a kasar Sin, ya ce kasar Sin babbar aminiyar hadin gwiwar kasar ta gabashin Afrika ce a yayin da kasar ke ci gaba da fafutukar yaki da bazuwar annobar COVID-19.

Ya ce kasar Habasha ta samu gagarumin tallafin daga gwamnatin Sin, inda aka samarwa kasar taimakon kayayyakin kiwon lafiya, da shirya taron musayar kwarewa na kwararrun masana kiwon lafiya, da kuma tallafin kai tsaye daga kwararrun masanan lafiyar kasar Sin.

Toga ya fadawa Xinhua cewa, kasashen biyu sun gudanar da ayyuka da dama dake shafar yaki da COVID-19 tare, da suka hada da musayar nasarorin da kasar Sin ta samu a yaki da COVID-19 domin taimakawa kasar Habashan a yakin da take yi da annobar ta COVID-19.

Kawo yanzu, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Habasha ya kai 55,213, bayan samun sabbin mutane 804 da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Juma'a, kamar yadda hukumar lafiyar kasar ta sanar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China